Amfanin Wajen Ga Lafiyar Jikin Dan Adam
Mafi yawan mutane sun fi sanin amfanin Gamba wajen, a yi alkalami da shi, don rubutun allo. To amma Gamba na da sauran amfani wajen kyautata lafiyar jikin dan adam.
Ga Wasu kaɗan daga cikin Amfanin Gamba:
Tana Maganin ciwon Hauka:
Idan aka hada saiwar Gamba da kuma furenta, sai a tafasa, a sa zuma. Idan ya huce sai a dinga sha. Yana magance cututtukan rikicewar kwakwalwa da cututtukan da ke fitar da mutum daga hankalinsa.
Tana Magance Cututtukan da ake iya dauka yayin saduwa.
Idan aka hada saiwar Gamba da kuma furenta, sai a tafasa, a sa zuma, a dinga sha da duminsa. Yana magance dukkan cututtukan da ake iya dauka yayin saduwa, kamar cutar sanyi da kanjamu da dai sauransu.
Tana Sanyawa Ma’aurata Sha’awar Jima’i.
Saiwar gamba, idan aka tafasa aka sha, tana karawa ma’aurata inganci wajen sha’awar kwanciyar aure (Jima’i).