Yadda Ake Amfani Da Lemon Tsami Wajen Magance Asiri Ko Shiri
Nasan cewa mutane da yawa sun san amfanin lemon Tsami kuma suna sonsa kuma suna amfani dashi. Wasu kuwa basu sonsa kasancewar shi abune mai tsamin gasake.
Hakan tasa wasu kan kalleshi a mazaunin marar amfani a garesu, to insha Allah yau Shafin Alummar Hausa Yasamo muku wasu muhimman aiyuka da lemon tsami kanyi a jikin dan adama.
Ina fata zaka tattara hankalinka/ki Sosai don amfana da abin kuma don Allah ayi kokarin turawa yan uwa suma su samu su amfana kar yazama kai kadai.
Wadannan sune kadan daga cikin abubuwan da wannan lemon tsami kanyi.
•Asiri (Sihiri)
•Baki
•Kambun baka
•Kulli
•Turbuda
•Ko wanda Aka turawa aljanu (Iskoki)
•Hau ko Hawa’I
Ko kuma duk wani abu da yadanganci hakan.
Zaa nemi Lemon tsami guda dari da sha uku (113) sai a yankashi gida biyu sai a samu kwano kokuma kwarya a zubashi a ciki gabadaya.
Sai a kawo ruwa mai yawan gaske azuba a ciki, sai kuma a karanta wandannan ayoyi a tofa a ciki:
•Falaki dari da goma sha Uku (113).
•Nasi dari da goma sha uku (113).
YADDA ZAAYI AMFANI DASHI
Lokacin da zaka kwanta saika debi ruwan daka zuba wannan lemon tsamin a wani abu mai kyau sai kaje kayi wanka a wuri mai kyau kokuma kashafe jikinka dashi baki daya.
Bayan ka gama saika kwanta haka zaka dingayi
Isha Allau cikin kankanin lokaci zaka samu sauki da yarda Allah.
Ayayin baccin naku ku dinga lura da irin Mafarke mafarken da zaku dinga yi.
Allah ya temaka ya kuma sa a dace da wannan ameen.