Kannywood

Nine mutum na farko Dana Fara YouTube series a masana’antar kannywood a shekarar 2018 (Rayuwar masoya) – Director Mujahid M Soja

Nine mutum na farko Dana Fara YouTube series a masana’antar kannywood a shekarar 2018 (Rayuwar masoya) – Director Mujahid M Soja

” Rayuwar masoya ya Kafa tarihin da kullin idan naga masana’antar kannywood Tayi busy kowa Yana fita production sai naga 90% na production din target dinsu YouTube ne Tabbas kullin Ina jin Dadin yadda na zama silar juya wannan masana’anta ta hanyar kawo dabarar YouTube series

A yanzu Kuma na Matsu naga an fito da wata sabuwar hanyar da masana’antar zata Kara dogara Akai saboda YouTube ya Fara bani tsoro a yanzu duba da yadda naga anayin sababbin SERIES a kalla guda 30 ko 50 a shekara daya amma dakyar ne ake iya samun guda biyu su tashi har masu aikin su amfana

Ni dai a iya sanina Babu cigaba a duk masana’antar da a kalla ake iya producing series guda 50 a shekara daya Amma dakyar guda biyu ko uku suke maida kudin su har suci riba

Idan nace su maida kudi ba Ina nufin ka zuba 5 million ka sami 5 million din ba kawai saboda film ya wuce ribar ri6anya kudi maganar Cin riba ake masa GA Wanda yasan yadda ake hada Hadar film ta Duniya

Idan muka tsaya mukai dogon nazari ya kamata mu gane iya YouTube bazata rike kannywood ba ya kamata tunanin mu ya Fara Nisan zango akan hanyoyin Daya kamata ace an Kara samarwa masana’antar mafitar da zata dogara Akai

Babu wata film industry a Duniya Dana Santa wacce ta dogara da YouTube Banda kannywood!

Dan kannywood da kayi masa maganar cigaba sai kaji Yana Netflix ko amazon, Ni a tunanina ba iya wadan Nan platforms dinne abin kalla ba Amma idan aka zurfafa tunani Tabbas zamu iya kirkiro Abinda Babu wata masana’anta a Duniya da take da irinsa ko Kuma ta raja’a akansa!

toh Amma ta yaya? Kuma su waye masu samarwar?

Ni dai anawa gajeran tunanin na Gano za’a iya samar da cigaba Sosai idan ya zamana duk wani Dan kannywood yaji a ransa cigaban masana’antar itace a gaban duk wani burinsa sannan idan ana zancenta ya ajjiye duk wani Abu a ransa ya fuskanci cigabanta

Masu samar da cigabanta Kuma ko hanyar da za’a Nemo bai ta’allaka kadai akan jagororin masana’antar ba kowa Yanada damar bawa zuciyarsa da kwakwalwarsa damar tunani nasan Kuma zamu iya!

Fatana ubangiji Allah ya cigaba da Sanya Albarkarsa cikin wannan masana’anta Mai Albarka manyan mu dake cikinta ubangiji Allah ya cigaba da inganta rayuwar su Kuma yadda suke da kyakkyawan fata akan wannan masana’anta Allah ya biyasu da mafificin Alkhairi

mujahidmsoja✍️

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu