Kannywood

Gwamnatin Kogi Ta Amince Da Karin Shekarun Ritaya Ga Malamai

Gwamnatin Kogi Ta Amince Da Karin Shekarun Ritaya Ga Malamai

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa amincewar ta biyo bayan amincewa da dokar ritayar malaman makaranta a jihar Kogi da kuma batutuwa masu alaka da Hakan, tun 2022 Kuma a ranar Alhamis din nan majalisar dokokin jihar ta amince da Hakan.

Kakakin majalisar, Matthew Kolawale, ya ce bayan amincewa da kudirin dokar, yanzu malaman jihar za su dinga yin ritaya idan sun kai shekaru 65 da haihuwa, ko shekarun aiki 40.

Dokar ma’aikatan gwamnati ko kuma duk wata dokar da ta bukaci mutum ya yi ritaya daga aikin gwamnati yana da shekara 60 ko kuma bayan Ya shafe shekaru 35 yana aiki ba za su shafi malamai a Kogi daga ranar da aka fara wannan doka ba,” inji shi.

Rahotanni na nuna cewa, A shekarar da ta gabata, Adadin mutanen da suka rasa matsugunansu ya kai miliyan 71.1 a fadin duniya saboda tashe-tashen hankula kamar yakin Ukraine da Iftila’in da sauyin yanayi ya haifar kamar ambaliyar ruwan damina a Pakistan, a cewar, wani rahoton da aka wallafa a ranar Alhamis.

Kamfanin Dillancin Labaran Reuters ya ruwaito cewa, Cibiyar Kula da adadin masu neman mafaka a Geneva (IDMC) ta ce adadin ya karu da kashi 20 cikin 100 tun daga shekarar 2021, inda ba a taba samun irinsa.

IDMC ta ce kusan kashi uku cikin hudu na mutanen da suka rasa matsugunansu a duniya na rayuwa ne a kasashe 10 da suka hada da Syria, Afghanistan, Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, Ukraine da kuma Sudan sakamakon rikice-rikicen da suka haifar da gagarumar gudun hijira a shekarar 2022.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu