Kannywood

Har kebe Matata na yi a wuri Daban Domin Rashin Zama Lafiya da Yan uwana Da yarana Adam A Zango..

Har kebe Matata na yi a wuri Daban Domin Rashin Zama Lafiya da Yan uwana Da yarana Adam A Zango..

Fitaccen jarumin Kannywood, Adam Zango ya wallafa bidiyoyi yana bayyana yadda suke cikin tsaka mai wuya shi da matarsa.

A cewarsa, ya fito ya yi bayani ne kada a cigaba da kallonsa a matsayin auri-saki, don haka zai wanke kansa daga zargin jama’a.

KU KARANTA: Na so in fara fim a ɓoye kafin iyayena su amince min, Sa’a ta shirin Labarina.

Ya ce tun farkon aurensu da matarsa ya ce mata ba ya son harkar soshiyal midiya, kuma ta fara bi yanzu ta sauya.

A cewarsa ta wallafa wani bidiyo tana kwasar rawa tare da lalle a jikinta wanda hakan ya sa ya ce ta tafi gidan iyayenta.

Bayan tafiyarta ya bukaci a amshi wayarta don ba ya son rike wayar da ake sanya data don gudun abinda zai je ya dawo.

Ya ce ta kai watanni uku a gida kuma matsawar bata cika sharuddansa ba za su samu gagarumar matsala tsakaninsu.

Ya shaida yadda yake samun rashin jituwa tsakaninta da yaransa da ‘yan’uwansa, inda ya kebe mata gidanta daban wanda za ta zauna ba tare da ta yi alaka da kowa ba.

Amma bisa yadda yake bayani, ba wannan bane makasudin samun matsalarsu ba, al’amuran kafar sada zumunta ne za su janyo gagarumar matsala tsakaninsu.

Dama an yi wa Jarumin shaida auri-saki, kasancewar ba ita bace matarsa ta farko ba, ya auri matarsa ta farko sannan ya auri maman haidar, babban dan sa, wacce Abayas rabuwarsu ta dawo fim.

Ya kuma auri wata mata daga kasar Kamaru, wacce a lokacin suka sha soyayya amma daga bisani zaman bai yi tsawo ba.

Ya auri tsohuwar jaruma Maryam AB Yola, wacce bata kai ga haihuwa ba suka rabu. Bayan dawowarta sana’ar fim kuma ba dadewa ta yi aure.

Daga ita ne sai wannan Safiya Chalawa da suke zaune yanzu kuma rikici ya barke tsakaninsu. Duk da dai ana cewa mai daki shi ya san inda ke yi masa yoyo, muna fatan Ubangiji ya daidaita su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu