Kannywood

Jerin jaruman kannywood da suke da saurin fushi da abinda yake sa su saurin fushi.

Ko wanne dan Adam yana da abinda yake sa shi saurin fushi, hakan yasa ayau muka kawo muku wasu daga cikin jaruman kannywood da suke da saurin fusata idan aka musu abinda basa so.

ALI NUHU

Nasan wasu mutane zasu yi mamakin ganin Ali Nuhu cikin jerin jaruman kannywood da suke saurin fushi kasancewa baya yawan fitowa a finafinai mai saurin fushi, wannan ba abin mamaki ba ne domin hausa sunce dan adam 9 yake bai cika goma ba,

Jarumin mai farin jini wato Sarkin kannywood Ali Nuhu a wani tambayar da Jaridar bbc hausa cewa wani dabiar shi ne yafi tsana, sai ya bada amsa da cewa saurin fushi, wannan shi ya kara tabbatar da cewa jarumin akwai shi da saurin fushi. Domin shi jarumin mutum ne da yake so a mutunta shi da kuma ganin girmanshi.

Domin idan ka tsaba nishi lallai zaka ga fusata cikin fushi, ko kwanakin baya ya maka wani jarumin kannywood din kotu, ba komai bane ya jawo hakan illa fusatar da yayi na zargin bata masa suna da aka yi, hakan yasa jarumin baya saka kanshi kan abinda ba’a sanya shi ba, saboda saurin fushin da yake da shi.


Shi dai wannan jarumin Ali Nuhu yasance mutum ne mai saukin kai ga taimakawa ƙananan jaruman kannywood, baza a iya fadin iya adadin mutanen da ya samowa aiki a masana’anta kannywood ba.

ADAM A ZANGO

adam a zango ya kasance mutum ne mai saurin fushi, bazai taba raga maka ba duk alakarka da shi idan ka masa kaza fi, domin jarumin akwai tabbacin cewa yana daga cikin abubuwan da yafi tsana a rayuwasa shine kazafi, ansha yi jarumin kazafin luwadi neman mata da sauran su,

a duk lokacin da aka masa irin wannan kazafin anan take ake ganin fusatarsa a zahiri har Al’amarin yakan iya kaishi rantsuwa da Alkur’ani mai girma domin kare kansa daga kazafin da ake masa. Ya kasance mutum ne da baya sakawa bakinsa linzami idan ka yi mishi ba dadi zai fito ya fada maka, Idan kana rayuwa da Adan zango kaji tsoron yi mishi kazafi domin anan zaka fusatarsa.


Amma kusan kowa ya sani Adam a zango mutum ne na mutane da yake da yawan fara’a da mutane, ga kuka taimakon marasa galihu.


 

HADIZA GABON

Kyakkyawar jarumar haifaffiyar kasar gabon da take yawan kiran kanta mutumiyar kirki. Hadiza ta kasance mutum ce mai tsaurin fusata, domin duk mai bibiyar harkar kannywood yasan da haka, saurin fusatar Tata ne yasa,

kwanakin baya da ta dauki mummunar mataki kan wata jaruma a kannywood da ita Hadiza gabon din ta zargeta kan tayi rubutu a kanta kan abinda ya danganci madugo, kenan ita wannan jarumar zamu iya cewa TSANI mutum ya bata mata suna a idon duniya domin yin hakan yana saurin fusatar da ita jarumar Hadiza gabon.


Kamar yadda take kiran kanta mai kirki tabbas hakane jarumar akwai kirki, domin kuwa ansha yada hotunanta shafukan sada zumunta tana taimakawa nakasassu da marayu da sauran mabukata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu