Kannywood

Gaskiyar magana akan Auren Ado Gwanja da Momme Gombe

Gaskiyar magana akan Auren Ado Gwanja da Momme Gombe.

Yanzu-Yanzu ne wasu hotuna suka karade shafukan sada zumunta na Facebook hade da Instagram inda akaga shafukan da suka shafi bangaren kannywood sun wallafa kyawawan hotunan Ado Gwanja da Momme Gombe Wanda sunyi matukar kama dana Aure.

Sai dai kamar yadda kuka sani shafin mu na labarai.com.ng bama kwan mu saida zakara,mun bi duk wasu hanyoyi domin tabbatar da sahihancin hakan saida mun tuntubi mutanan biyu basa kusa basu daga kira ba.

Hakan keda wuya sai muka bi tsarin yadda irin abubuwan da suka saba faruwa makamantan hakan.

Da Farko munyi duba da Tufafin Ado Gwanja din ba sabo bane,domin da kayan ya dauki hoton tallar Album dinshi daya saki a kwanakin baya na Amada.

Na biyu,cikin masana’antar kannywood ana yawan samun iri iren hakan sai daga baya ayi bayani bayan hotuna sun dauki hankulan mutane,yawancin hakan yana zama ko wajen daukar wani sabon shiri ko bidiyon waka ko kuma tallar wani gurin hakan.

A ƙarahe dai wannan hotuna sun kasance na ɗaukar film ɗin ALAQA SERIES ne bana Auren Suba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu