Kannywood

Innalillahi Waina ilaihrajiun Mawaki Kwankwasiyya Tijjani Gandu Ya Hadu da Hatsarin Mota

Innalillahi Waina ilaihrajiun Mawaki Kwankwasiyya Tijjani Gandu Ya Hadu da Hatsarin Mota

Fitaccen Mawakin Kwankwasiyyar nan a Jahar Kano watau tijjani gandu wanda yayi Wakar Abba gida gida Allah Ya jarabce shi da hadarin mota.

Mawakin Yayi fice ne tun a lokacin da yayi wakar abba gida gida a shekarar 2019, Wakar tayi Matukar tashe kuma tana daya daga cikin dalilin daya sa mutane suka kara sanin Dan Takarar watau abba gida gida a lokacin.

Shafin Kannywood Exclusive a kafar Sadarwa na Instagram sune suka wallafa labarin a shafin nasu inda suka bayyana kamar haka: Mawakin Kwankwasiyyar tijjani gandu ya hadu da ibtilain hadarin mota a jiya da daddare a yanzu haka yana kwance a asibiti domin ceto Lafiyar sa.

A karshe muna masa Addu’a Allah ubangiji Ya bashi lafia yasa kaffara ne Ameen

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu