Kannywood

Tattanawa da Hadiza Gabon akan rayuwarta mai mahimmanci da baku sani ba, zai baku mamaki

FATANKI NAN DA SHEKARA 5

Aure, haifuwa da arziki insh’Allah

MINTI NAWA KIKE DAUKA KINA KWALLIYA?

Bancika yin kwalliya ba, wannan ma da nayi saboda za’a yi interview da ni ne.

WANENE SAURAYIN KI A KANNYWOOD

Hmm duk yan uwana ne a kannywood

RADE RADIN DA AKE YADAWA GAME DA KE

Ta girma ta tsufa bata yi aure ba, bata son tayi aure wayannan abubuwan su na daya daga cikin abubuwan da aka fi fada.

YA KIKE JI IDAN AN ZAGE KI

Wani lokaci nakan yi dariya wani lokaci nakan yin kuka, sanna wani lokacin nakan ramawa.

KAYAN KI KALA NAWA NE

Ban sani ba

WANI TUFAFI KIKA FI SO KI SAKA

Nafi sa dogayen riguna sannan nafi son atamfa.

WANI FILM DINKI NE SUNANSHU YA BIKII

Wasu tsayin ana cewa yar maye amma hadiza gabon din ya danne duk wani sunan finafinaina

KI FADA MANA ABUBUWA UKU GAME DA KE

Ni mutumiyar kirki sanna 9 ce bata cika 10 ba dama ance dan adam ajizi ne, ina kuskure ina laifi sannan na uku zan iya maimaita mutuwar kirki.

TAURARUWAR DA KIKA FI SO

Akwai wata a america tana yin programmes tana taimakawa al’umma ta hanyoyi da dama.

WANI WAKA CE KIKA FI IYAWA

Sai dai nace mawaka su yi hakuri babu wata waka da ta tsaya min akai,

sai dai wani lokacin idan aka saka waka zan iya binta idan aka katse kuma bazan iya binta ba.

FINAFINAI NAWA KIKA YI

Bazan fada maka iya finafanan da nayi ba.

TALAKA KOMAI KUDI KIKA FI SO

Hhhhhhhh ehh duk wanda Allah ya bani.

WACECE AMINIYAR KI A KANNYWOOD

Duk yan kannywood kawaye nane.

SHIN ZAKI BARI MIJINKI YAYI MIKI KISHIYA

Ko da baka yarda ba Allah ya bashi ikon ya auri mata hudu, to me yasa zaka hana abinda Allah ya halatta sai dai ka yi hakuri

IDAN BAKYA YIN FIM ME ZAKI YI

siyar da kaya Ko mamalkiyar shagon abinci da saura .

A WATA NAWA KIKA KOYI YAREN HAUSA

Baka iya gane iya lokacin da kake koyan yare, wasu kalmomin zuwa maka kawai suke sanna su karu.

Daga lokacin da nazo a lokacin na koya kuma har yanzu ina kan koya.

WACCE CE BOYAYYIYAR BAIWARKI

Babu

WANE NE BABBAN JARUMIN KI A KANNYWOOD

Shi ne Rabilu Musa dan Ibro Allah ya gafarta masa.

WANNE FIM DINKI KIKA FI SO

Kamar yadda nasha dukkan finafinai ina son su, shi film wani abu ne da ake kawo maka ka karanta watakila a kalla an kawo maka guda goma ne sai ka zabi guda daya to wannan wanda ka zaba shine kafi so ne, saboda yawancin finafinan da nayi ina son su saboda sai na zabe su nayi su.

DA WAYE KIKA FI SO A HADA KU A FILM

Ya dangata da producer da yanayin fim din, gaskiya bani da zabi nidai kawai abinda nake gani duk wanda aka hada ka shi kayi kokari kaga ka bada abinda ake so.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu