Kannywood

Matata Ummi Rahab ta tsallake rijiya da baya – Inji Lilin Baba

Mawaki Lilin Baba ya yi posting mai zafi da ya janwo cece kuce gami da muhawara a kafafen sadarwa na zamani.

Mawakin ya saki wani hotonsa ne tare da matarsa Ummi Rehab a shafinsa na Instagram inda ya yi wani rubutu cikin harshen Turanci da ke cewa “My wife-Ummi Rehab, has really dodged a bullet. Thank God!”, ma’ana “Alhamdulillah! Matata Ummi Rehab ta tsallake rijiya”da baya

Hoton Posting ɗin da Lilin Baba yayi.

Ana ganin cewa Lilin Baba ya yi habaici ne ga Adam A Zango a wancan rubutun mai dauke da hoton nasa da Rahab, bayan da jarumi A Zango ya sanarwa da duniya halin da a ke ciki tsakaninsa sa da matarsa Safiyya.

Lokacin da Zango yake bayani akan aurensu

Idan ba a manta ba Adam Zango dai shi ne wanda ya raini Ummi Rahab a masana’antar Kannywood, wanda daga karshe suka samu sabani har aka raba gari tsakaninsu, daga irin zargin da Ummi ta yiwa Zango kafin rabuwar ta su, shi ne cewa ya nemeta da aure wanda ita kuma ta ki yarda.

Wasu da dama na yiwa Adam Zango ganin mutum mai yawan auri-saki, bayan da ya rabu da matansa a karo na hudu, har da matarsa ta yanzu, wanda ya shelanta cewa suna daf da rubuwa, wanda a halin yanzu haka Safiyya na gidan iyayenta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu