Kannywood

Tattaunawa da Daddy hikima akan rayuwarsa da baku sani ba.

TAKAITACCEN TARIHIN KA?

Sunana na yanka Adam Abdullahi Adam wanda aka fi sani da a Abale sannan ana kirana da Daddy hikima an haife ni a garin kano.

YA AKA YI KA SHIGA MATSANA’ANTAR KANNYWOOD?

A farko dai ban shigo kannywood a matsayin Actor ba, na shigo ne a matsayin designer, amma ni burina na so na zama director.

ME KA KARANTA A MAKARANTA?

Na karanci kiwon lafiya, ni nurse ne.

AINA KAKE AIKI?

Ina aiki a asibiti, amma saboda yawan ayyuka da nake da su a kannywood, sai da kawai ina zuwa watarana domin taimako.

KANA DA AURE?

A’a bani da aure, In Allah ya kawo wata rana za’a yi, aure da mutuwa duk na Allah duk ranar da yace zaka yi to sai kayi shi.

KANA DA BUDURWA?

Eh, ina da shi, kuma inch’Allah idan muka shi aure zan gayyace ku.

AN TABA MAKA WANI KYAUTA DA KAJI DADI SOSAI?

Eh, kyautar mota da rarara ya bani, naji dadin sa sosai.

MENENE BABBAN BURUNKA?

Watarana na zama soja shi yasa na shiga nurse, ina son soja sosai.

WANNE ABINCI KAFI SO?

Kayan ciki, ina son kayan ciki da ganda

WACE CE GWANAR KA A KANNYWOOD?

Aisha Aliyu Tsamiya

MUN GODE DA TATTAUNAWA DA KAYI DA MU.

Nima na gode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu