Kannywood

Bani Da Budurwa Amma Nan Da Wata Biyu Zanyi Aure Cewar Presdo Jarumin Film Din Labarina

Fitaccen Jarumin Kannywood Kannywood Wanda A Yanzu Yake Taka Muhimmiyar Rawa Acikin Shirin Film Dinnan Mai Dogon Zango Wato Labarina.

Jarumin Wanda Akeyi Masa Lakabi Da Presdo Acikin Film Ya Bayyana Cewa Bashi Da Tsayayyiyar Budurwa, Amma Duk Da Haka Bazai Wuce Wata Biyu Ba Zai Yi Aure.

Ga Masu Bibiyar Shirin Film Din Labarina Mai Dogon Zango Jarumin Ya Kasance Dan Masu Kudi, Sannan Kuma Mai Nuna Takama Da Arzikin Da Yake Dashi.

Sai Dai Kuma Aka Jarabceshi Da Soyayyar Wata ‘Yar Talakawa Acikin Film Din Wato Sumaiyya Wanda Shine Sunan Da Ake Kiranta Acikin Film Din, Amma Sunan Da Akafi Saninta Dashi Shine Nafisat Abdullahi.

Jarumin Mai Suna Presdo Acikin Shirin Film Din Labarina, Ya Bayyana Hakane A Yayin Hirarsa Da Shafin Garkuwar Arewa Na Instagram Yadda Ya Bayyana Musu Cewa Shi A Yanzu Bashi Da Tsayayyiyar Budurwa, Amma Duk Da Haka Bazai Wuce Wata Biyu Ba Zai Yi Aure.

Haka Zalika Jarumin Ya Bayyana Yadda Film Din Labarina Ya Kara Masa Mabiya Da Masoya A Duniya, Duba Da Yana Taka Muhimmiyar Rawa Acikin Film Sannan Kuma Yana Birge Masu Kallo.

Ga Bidiyon Da Akayi Hirar Dashi Sai Ku Kalla Kuji Cikakken Bayani Daga Bakinsa.

Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaco Akan Wannan Magana Da Jarumin Yayi Nacewa Zai Yi Aure Nan Da Wata Biyu, Duk Da Bashida Tsayayyiyar Budurwa.

Sannan Zamu So Ku Watsa Labarin Nan Domin Yaje Kunnen Masoyansa, Saboda Su San Jaruminsu Ya Kusan Angwancewa, Kada Ku Manta Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu