Kannywood

Tattaunawa Jaruma Fati Muhammad Alan Rayuwar Ta Da Baku Sani Ba. Ina Son shinkafa da wake

MINTI NAWA KIKE KWASHEWA WAJEN YIN KWALLIYA ?

Toh gaskiya ina kwashe kamar minti 3-4.

WANE NE SAURAYIN KI NA FARKO ?

Saurayina na farko a garin su maman mu ne a garin yobe sunan shi nura.

WANE ABU NE KE SAKI FARIN CIKI ?

Toh idan kanason farin ciki na shine kayimin alkawari kuma ka cika min.

WANE ABINCI KI KA FI SO ?

Shinkafa da wake da salak da yaji.

WACE KYAUTA CE AKA TABA BA KI DA BAZA KI MANTA BA ?

Ehh, Akwai wani award da aka taba bani a makaranta wannan naji dadin shi sosai. Sannan da taron Aure na.

WACE TAMBAYA KI KA GAJI DA AMSAWA?

Tambayar itace Fati muhammed mai yasa kika bar fim.

WANE FIM NE KIKA FI SO CIKIN FINA-FINANKI ?

Ehh to dukka fim din danayi ina alfahari dashi amma nafison fim din TSANGAYA.

WACE CE BABBAR KAWARKI ?

Amina Muhammad.

WANE JARUMI KI KA FI SO A HADA KU A FIM TARE ?

To lokacin da nake fim yan kallo ko ban fadi ba yan kallo sun riga sunsan nafi dacewa da Sarki Ali Nuhu saboda Ali nuhu idan kana fim dashi to shi da Gaske yake.

YA AKA YI KIKA FARA FIM ?

Toh a takaice dai ta dalilin kallon wani fim ne mai suna KI YADDA DANI Wanda ibrahim Mandawari ya dauki nauyinsa.

to tin daga wannan lokacin nafara sha’awar yin fim.

BAYAN FIM WACE SANA’A KIKA FI SO ?

Toh ni gaskiya ina son Sana’ar saye-da-sayarwa ta shago ko kuma restaurant.

KINA DA WATA BOYAYYIYAR BAIWA ?

Toh gaskiya ni bani da wata baiwa sai dai kaga ni ba fulatana ce kamar yanzu idan naje gaban Saniya zan iya

tatsar nono na mayar dashi kindirmo Wanda shine gadona. Kaga ba kowa ne zai iya ba toh inaga itace baiwar da nake.

WACE KARYA AKA TABA YA DAWA GAME DAKE ?

Kwarai da Gaske akwai lokacin dana fara fim sai aka fara yada karya fati Muhammed ta mutu.

HARSUNA NAWA KI KA IYA ?

Ehh, inajin yaran Hausa,Fulatanci, sai kuma Turanci, kadan-kadan.

ME YASA KI KA SHIGA SIYASA ?

Toh Ra’ayi da kuma idan Allah yace zakayi abu tin kafin kazo duniya saika yishi.

MENE NE BABBAN BURIN KI A YANZU ?

Babban burina shine Allah ya rufa min asiri naga nayi Aure na rufawa kaina asiri.

TA WACE HANYA KIKE GANIN ZA’A SHAWO KAN MATSALAR FYADE ?

Toh ni ina ganin mu iyaye mata mu zamu kiyaye ma’amalar ‘ya’yanmu da waye yake daukar su koda dan uwanka ne saboda sanin mutum sai Allah.

TA WACE HANYA KIKE GANIN ZA’A SHAWO KAN MATSALAR TSARO ?

Yadda za’a SHAWO kan wannan matsalar shine muna da matsalar kayan aiki dakuma rashin tsaurara hukunci.

AN TABA YIN GULMAR KI TA DAWO KUNNEN KI ?

Ehh, sosai ma dan ko yau dana tashi saida naji anyi kuma ni baya damuna saboda na isa ne kuma ni takaina nake.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu