Kannywood

Tattaunawa Da Jaruma Aina’u Ade Akan Rayuwar Ta Da Baku Sani Ba. Ina Jin Daɗi Tsegumi

WANE IRIN TSEGUMI KIKA FI SO ?

Kinsan mu mata hanji ne wannan tsegumi idan bamu yiba sometimes bamajin dadi mun iya tsegumi sosai bare mu irin mu ko da ido sainayi anyi tsegumin kenan ai.

WANE ABINCI KI KA CI DAYA BATA MIKI CIKI ?

Ni abincin da yake bata min ciki idan nasha gari ko naci teber shine kawaii baya dacewa da System din jikina.

ME KIKA TABA YI DA HAR YANZU YAKE BAKI DARIYA ?

Ahh, kullum ina cikin abin dariya ni ai ko jiya ma nayi wani ina cikin bacci idan na Tina dariya nake.

Akwaii inda nake aiki office din mu to akwai wata inyamira ta takura min saina warware mata irin nawa juju din to yadda muka yi ni ina hooo ita tana dooo idan na Tina abun sai abin yayi tabani dariya.

WA KIKA FI SO A JARUMAN KANNYWOOD ?

Ni ba’a burgeni nifa abu idan ba harka na bane bana sanin yananan ko bayanan.

WANE ABU MASOYIN KI YA TABA YI DA YA BAKI MAMAKI ?

Hmm, ni masoyi ehh to may be lokacin da yarinta da baka mallaki hankalin kanka ba ni soyayyata

idan ina sonka tiryan-tiryan so sosai ba miss ba kwana-kwana kana yimin rashin gaskiya sau daya toh an huce gurin kara waiwaya baya gaskiya.

AKWAI CUTAR DA KE DAMUNKI ?

ehh, gaskiya akwai ina fama da hawan jini sannan kuma sometimes sugar na yana hawa amma hawan jinin yafi karfi.

ABUN DA BAKYA SO AYI MIKI ?

Na tsani ayimin karya bana karya.

WACE DABI’A CE TA ZAME MIKI JIKI ?

Ni kaina bansani bah sometimes bana gane kaina wani lokacin in birkice wani lokacin inyi daidai ganinan dai nima bana gane kaina.

WAYE SAURAYIN KI A KANNYWOOD ?

Ehh, Wannan ai Babbar magana kika tambaye ni babu kowa ni kadai nake yawo bana dashi.

CHATIN KO MAGANA TA WAYA ?

Ni banayin sai ayi min magana a WhatsApp sau 100 bana reply.

DA BAKI ZAMA ‘YAR FIM BA WACE SANA’A ZA KI YI ?

Sana’ar sayar da kaya kamar leshi, anything about bride hakan nan ina planning inyi shagon a kano.

WANE ABINCI KI KA FI SO ?

Ina son moimoi.

MAI YAFI WAHALA A RAINON YARA ?

Ni ba wani wahala a rainon yara ni a yanzu ma da Allah zai bani miji nayi aure ina sha’awar naga na koma haihuwa inga ina rainon biyu-biyu ina burgeni saboda idan ina rainon baby nafi tsafta.

KANO KO OSUN ?

Up course Kano mana ni da aka Haifa a nan na girma fah idan naje OSUN sainaga mutanen kamar ba.

WACCE TAMBAYA CE BAKYA SO ?

Tambayan kwakwa ka ganni kaga abu ka tambaye ni kace wannan wanna kalane kuma kai Kana gani irin wannan tambayar yana Kular dani.

Kasance da *Manuniya.com domin samun sabbin labaran kannywood dan samun nishadin Ku . Saboda jin dadinku shine namu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu