Kannywood

Gwamnatin Kano ta ja kunnen jarumar Kannywood, Teemah Makamashi

GWAMNATIN Jihar Kano ta gargaɗi jarumar Kannywood, Teemah Makamashi, da cewa ta san iyakar ‘yancin faɗar albarkacin bakin ta. 

Hakan ya biyo bayan maganar da ta yi a cikin wani guntun bidiyo da ta wallafa a TikTok a ranar Alhamis, 9 ga Fabarairu dangane da batun shari’ar jarumar TikTok Murja Ibrahim Kunya wadda a yanzu ta ke tsare a gidan yari na Kurmawa a cikin garin Kano a bisa umarnin kotu.

Teemah dai ta ce ta shiga ta fita ta yi ‘yan abubuwa, kuma za a sako Murja cikin kwana biyu.

Ta ce duk da yake abin da Murja ta yi ba daidai ba ne, amma ta haɗu da wasu manyan, don haka za a sake ta.

Sai dai mai magana da Hukumar Kula da Kotuna ta Jihar Kano, Malam Baba Jibo Ibrahim, ya musanta iƙirarin jarumar sannan ya nemi da ta janye maganar domin har yanzu Murja dai ta nan nan ta na ci gaba da zaman ‘yar gari a kurkuku.

Sannan ya gargaɗe ta da ta sani cewa shi fa haƙƙin tofa albarkacin baki ya na da iyaka, don haka ta daina cusa kan ta inda za ta tsallake iyakar ta don gudun jefa kan ta cikin wani hali.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button