Kannywood

Tattaunawa Jarumi Shehu Hassan Kano Akan Rayuwar Sa Da Baku Sani Ba.

KANA YIN WAKA ?

Ni ina tinanin idan nace zanyi waka to gaskiya duka za’a yimin.

A WAKOKIN GARGAJIYA NA HAUSA WACCE KA FI SO ?

Dodo na cikin daji janare na Kan hanya jatau na cikin office to wannan wakar tana daga cikin wakokin da nake so na SHATA banda wakar BABA DIREBA.

WANENE GWANIN KA A MASU WASAN HAUSA.

Gwanina ya rasu domin ni gwanina bai huce Alhaji kasumu yaruba Allah ya jikansa dalilin da yasa kasumu yaruba yazama gwanina shine dalilin da yasa na samu sha’awar na shiga harkar fina-finan hausa.

KA TABA YIN SHAYE-SHAYE ?

Ehh to wato abin da yasa banason cewa na taba yin SHAYE-SHAYE to abu ne na yarinta ko kuruciya wato wiwi ce akwai wani lokaci Wanda har yanzu bana mantawa da lokacin daga nan ne nasan cewa gaskiya ina da karamar kwakwalwar da idan nace zanyi wannan shaye-shaye to zan kai kaina dawa.

Akwai lokacin da wani yayanmu ana ce masa Habulele yayi aure mutumin fage ne a nan bakin wafa dani da abokaina munje sai a kazo a na raba wiwi a Kan tire to gaskiya

an murzamin roll daya da suke kira nidai bankai da shanye waba daga nan ban kara sanin a ina nake ba sai naganni a Kan gado a gida a kwance ashe wai saida na samu kamar kwanaki 3 bansan a ina nake ba.

AN TABA MARINKA KA GA WUTA ?

Akwai wani mutum bagobare lokacin nan wani wai sarkin dima yana kidan dima wata rana munje kallon wannan wasan dimar sai kawaii naga wannan

bagobaren yayi tankol ya shafa mayi Kan yana kyalli ni kawai ba abun da yabani sha’awa sai in daki wannan kayi bagobare nazo ana rawa rawa ta dauki dadi

kawai na samu kanshi nabashi tassss wannan dukan da nayi masa da ya juyo ya ganni sai ko ya same ni yabani fesss ni da kaina nacewa abokaina na wajen a kashe mitre na dauka touch a keyi saboda irin abu buwan dana gani a cikin idona saiko aka fara dariya bagobare yayi mari wannan barin bazan taba mantashi bah.

WACE CE BUDURWAR KA TA FARKO ?

Wato wani abun da zai baka mamaki abokaina wanda muka taso dasu tare sun sanni babu abin da nake tsoro a duniya sama da mace a wannan lokacin idan za’aje wajan yarinya za’ayi ado da kwalliya amma ni idan za’ace gani nazo wajen wata zance to tana fitowa zan gudu.

Domin bansan dalili bah ni kaina bansan mai zance mata bah akwai wata har yanzu idan ta ganni sai tacemin gudajjen saurayi.

ME YAFI FARAN TA MAKA RAI ?

Ni babban abun da yake farantamin rai a rayuwa shine naga samari sun zama mutanen kirki abun da yasa na janyo wannan layin shine bansani bah ko akwaii wasu a bayanmu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu