Kannywood

Tattaunawa da mustapha naburaska akan rayuwarsa da baku sani ba, da kuma yadda ya shiga film

KA GABATAR DA KANKA GA MASU KARATU?

Sunana Mustapha Badamasi Naburaska.

AINA KA SAMU SUNAN NABURASKA?

Wata jaha ce a america da aka bani award kuma sai aka yi wani film mai suna Naburaska, film din zai kai shekaru 17 ko 18.

YAUSHE KA FARA FILM?

Na fara sana’ar film a 2001 zuwa 2002.

DA WANI FILM KA FARA?

Bazan iya tunawa ba.

KAI DAN ASALIN WANI STATE?

Ni dan jihar kano ne.

ZAMU IYA SANIN ASALIN SHEKARUNKA?

Shekaruna 35.

KANA DA MATA NAWA?

Ina da mata biyu.

SHIN KANA SON KA KARA WATA MATAR?

Eh ina da niyar yin hakan. Ina son na auri Hadiza Kabara.

YAUSHE ZAKU YI AUREN?

Sai lokacin da Allah ya ƙaddara.

KAI KAKE ZABAR YIN BARKWANCI A FINA-FINAI?

Bani nake zaba ba, kawai idan an ga na dace sai a saka ni.

AN TABA DUKAN KA DA GASKE A FILM

Eh, an taba yi min dukan gaske a film sau da yawa.

WA KA TABA DUKA A FILM?

Na taba dukan Tijjani Asase a film kuma yayi min korafin yaji zafi kuma idan an hada mu a wani film zai rama shi ma.

YA KAKE JIN YADDA MUTANE KE MAGANA GAME DA ‘YAN MASANA’ANTAR KANNYWOOD?

Ai mutane suna kallon mu, yanayin shigar mu da yanayin mu’amalar mu, bai sai mutum ya wahala wajen bayyana shi mutumin banza ba, duniya ce zata bayyana kai mutumin banza ne, idan kuma ka zama mutumin kirki ba sai ka wahala ba, duniya zata bayyana ka.

Abinda na sani shi ne majority din yan film ‘ya’yan malamai ne, ciki har da ni, duk abinda zai taba addini na da Al’ada ta ina kauce masa, sannan bazan iya yin abinda zai taba mutuncin iyalan mu ba.

KA CE MAHAIFINKA MALAMI NE KUMA KAI KUMA ALMAJIRI NE, IZUNKA NAWA?

Nasan abubuwa da yawa a cikin Alkur’ani daidai gwargwado.

BAYAN FILM AKWAI WATA SANA’A DA KAKE YI?

Ni dan kasuwa ne bayan kasuwancin Film kuma dan siyasa ne ni.

A WANI FILM NE KASHA WAHALA SOSAI?

Film din da nasha wahala sosai a cikin sa shi ne film din Basaja.

ME YA BA KA WAHALA A FILM ƊIN BASAJA?

Su na da yawa domin akwai wuraren da murya nake canjawa, wani wuri zan yi muryar maza wani wuri zan yi muryar mata, wani wurin kuma muryar malamai nake yi.

A FILM DIN GIDAN BADAMASI WACE CHARACTER CE TAFI BIRGE KA?

Character da yafi birgeni a gidan badamasi, shi ne character da nayi.

TA YA KAKE CANJA SALON MAGANA ZUWA TA ‘YAN DABA?

Yadda Mustapha yake canja muryar sa ko kuma yadda bazuka yake canja muryar sa, shine yanzu kana ji na canja murya ta ya koma irin ta ‘yan daba.

SU WAYE MANYAN ABOKAN KA 3 A KANNYWOOD?

Idan kace abokai 3 sun yi kadan, domin duk wanda yake da alaka da comedy abokina ne, producers, directers duka abokaina ne.

KA FADA MANA ABINDA IDAN KA TUNA SAI YA BAKA DARIYA?

Abinda idan na tuna yake bani dariya shi ne. Wani mugunta da na taba yi wa Bosho a lokacin da muke shooting,

na diɓo kudade da yawa na zuba a gabansa kusa da wani bafulatani nace ga kudin aikin ka, sai hankalin shi ya tashi ya fara zage-zage yana cewa “ni za’a tonawa asiri” to wannan abin ya ban dariya sosai.

KA IYA WAKA?

Ban iya waka ba.

AMMA A SERIES DIN GIDAN BADAMASI AN GANKA KANA WAKA?

Tabbas a Gidan badamasi na rera waka da jita, amma director shi yake fada min abinda zan fada a wakar.

WANENEN GONINKA A GIDAN BADAMASI?

Kwani na a film din gidan badamasi shine dankwambo.

ME YASA DAKWAMBO YA ZAMA GWANINKA?

Allah yajikan Rabilu musa dan-ibro idan yana acting yana min kama da shi.

KA FADA MANA BURIKA 3 DA KAKE SO KA CIMMA ANAN GAB?

Burika 3 da nake so na cimma a rayuwata ta duniya bai wuce kan sana’a ta ba, na farko gwamnati ta tallafa mana kamar yadda muke tallafa ma ta,

na biyu mu sami kyakkyawar tsari a masana’antar mu ta kannywood sannan mu samu kyakkyawar shugabanci, wa’yannan su ne manyan burika na a duniya.

ME YAKE SAURIN BATA MAKA RAI?

Ganin Almajirai akan titi, wannan yana bata min rai sosai.

GODIYA MUKE GAREKA?

Muma haka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu