Kannywood

Tattaunawa Da Jaruma Fati Bararoji Akan Rayuwar Ta Da Baku Sani Ba.

YAYA AKA YI KIKA SHIGA HARKAR FIM ?

toh, Kasan shi duk abin da Allah ya tsara saika ci abinci a ciki sai ya sameka.

MEYE AKE NUFI DA KAN-TA-WAYE A HARKAR FIM ?

Ehh, Wanda baya harkar fim idan yaji ance kan-ta-waye sai yace yar kauye.

Abin nufin shine idan farkon shigowar ka industry idan baka hadu da mutanen kirki ba toh shine ake nufi da kan-ta-waye.

WANE KIKA FI TSORO ? KADANGARE,BERA ?

Gaskiya nafi tsoran kadangare.

WACE TSOKANA AKE YI MIKI DA KINA YARINYA ?

Hhhh 🤣 Jan Kosai.

KIN TABA TSOKANA AKA YI MIKI DUKA ?

Abu daya da ban mantaba shine akwaii wani lokaci da nayi tsokana na gudu ashe ana target dina.

Bayan wani lokaci an aike ni kawai sai ta kamani saida na suma.

AN TABA MARINKI KI KA GA WUTA ?

Ehh, akwai lokacin da nae tsagi nayi fada kawai aka mareni saida naga wuta fuskata ta kumbura saida aka kaini emergency sannan na gudu Abuja.

KIN TABA AURE KIKA DAINA FIM ?

Aa, Dama ni bantaba aure ina fim ba tin kafin nafara fim nayi aure.

KINA SHEKARA NAWA AKA YI MIKI FIM ?

Ina shekara 13

WANE BURI KIKE SO KI CIMMA A RAYUWA ?

Burina shine Allah ya dauwamar dani a soyayyar Annabi Muhammad (S.A.W).

Sannan yakara mana kusanci dashi yasa mucika da kyau da imani Sai kuma Aure.

Kasance da *Manuniya.com domin samun sabbin labaran kannywood dan samun nishadin Ku . Saboda jin dadinku shine namu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu