Kannywood

Tattaunawa Jaruma Hadiza Kabara Wato Lantana Daɗin Kowa – Ina da tsokana da faɗa

A INA KIKA SAMU KABARA ?

Nasamo kabara tin asalin mijina wanda muka rabu dashi.

ME YASA KIKA SHIGA HARKAR FIM ?

Nashiga harkar fim ne ta dalilin kallon wani fim tin ina yarinta sunan fim din ALLURA DA ZARE.

KUNE ‘YAN MATAN DA AKE YAYI LOKACIN ?

Ehh, gaskiya lokacin da muka shiga babu “yan mata a ciki.

WANI ABU NE BA ZA KI MANTA BA A MAKARANTAR KWANA ?

Yes, a boarding school babu abin da ba’a yimin ba.

nayi secondary school a kano sannan na tafi boarding school nayi senior secondary school a boarding.

WAYE SAURAYINKI NA FARKO ?

Saurayina na farko shine wanda na Aura.

YAYA A KAYI KUKA BATA ?

Wannan abun da ya shafeni ne babu ruwan duniya.

KINA DA TSOKANA LOKACIN DA KIKE YARINYA ?

Ehh gaskiya ina da tsokana da fada.

WANE IRIN ABINCI KIKA FI SO ?

Ehh, gaskiya abincin da nake so suna da yawa amma nafison shinkafa da miya da salak da nama.

KIN TABA ZURAWA DA GUDU A WAJEN YIN FIM ?

Ehh, mun taba zuwa wajen wani shooting a kwaram so Location din da aka sauke mu babu wutar nefa.

Kawaii cikin dare sai mukaga ana gudu wai anga hulba matar miciji.

YAYA SUNAN KI NA TSOKANA ?

Toh sunana na tsokana da a ke fadamin DIJE.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu