Kannywood

Tattaunawa Da Mawaƙi Alan Waka Akan Rayuwar Sa Da Baku Sani Ba. Ina da Mata Huɗu

WACCE TAMBAYA KA GAJI DA AMSAWA ?

Tambayar da na gaji da amsawa itace wacce waka kafi so a cikin wakokin ka.

WACE AMSA KAKE BASU ?

Ni wakokina ba ina yinsu ne dan kaina bane ina yinsune saboda al’umma saboda fadakarwa.

KANA DA WATA BOYAYYIYAR BAIWA ?

Toh ai boyayyiyar baiwata ta Bayyana itace wannan Fasaha ta WAKA ta Bayyana.

WACCE KYAUTA CE BA ZAKA MANTA DA ITA BA ?

Toh gaskiya suna da yawa saboda na farko kyautar da a ka yimin ta AIKIN HAJJI 🕌. Wanda lokacin bani da ko kudin guzuri a kace natafi to wannan kyautar bazan taba mantawa da itaba.

KANA DA ALAQA DA MARIGAYI ABUBAKAR LADAN ?

Ehh, ina da alaqa dashi ta harshen hausa da addinin Musulunci amma shi Dan zaria ne ni kuma Dan kano ne.

WANE ABUN BAKIN CIKI NE BA ZAKA TABA MANTAWA DA SHI BA ?

To gaskiya suna da yawa daga ciki akwai mutuwar mahaifina, da wasu Kaka nina guda biyu, wannan babban abun bakin ciki ne.

MECE CE DANGANTAKARKA DA GOBIRAWA ?

To nafada a cikin waka ta nace gobir ne asalina. Masarautar gobir itace Masarautar kasar hausa wanda daganan kakana ya fito.

WAYE BABBAN ABOKINKA A CIKIN MAWAKA ?

To a gaskiya ina da abokai a cikin mawaka da yawa.

WANE ABINCI KAFI SO ?

To abincin da nake so shima dangin wake ne. ina son Dan wake, wake da shinkafa da salak.

KANA KALLON WASAN KWALLON KAFA ?

Ehh, ina kallo ina goyon bayan kungiyar Manchester.

YAYA ZA’A MAGANCE MATSALAR TSARO A NIGERIA ?

Hanyar da za’a Magance a bayyane take kwanakin baya naji dan majalissa yayi magana idan ba za’a Magance matsalar Tsaro ba to zaiyi resigning. so gaskiya dole ne a samar da matakan Tsaro kamar police, civil defence, army, da sauran su.

WAYE KWANINKA A MASU WAKA ?

Nafijin wakar DAN ANACE, DA SHATA,.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu