Labarai

Don Mijinki Ya yi Budurwa a Waje ba Wani Abin Tada Hankali ba ne inji Wata Matar Aure

Don Mijinki Ya yi Budurwa a Waje ba Wani Abin Tada Hankali ba ne inji Wata Matar Aure.

Don mijinki ya yi budurwa a waje, ba wani abin daga hankali ba ne inji wata ‘yar fim.

Wata jaruma a masana’antar shirya fina-finan kudancin Nijeriya Kudirat Ogunro da aka fi sani da Kudi Algbo ta shawarci matan aure da su daina tayar da hankali kan mazajensu, don kuwa su san da sanin cewa dole mazan na alaka da wasu matan a waje.

A cikin wata hira da jaridar MANUNIYA, jarumar ta ce a wannan zamanin, ya dace kowace mace ta san da sanin cewa idan mijinta na gida shu ne nata, amma da zarar ya fita waje ya zama na matan waje.

Ta kara da cewa kowace mace ya kamata san cewa akwai matan bariki da ke bibiyar mazajen da ke da aure. Kan haka ne ta ce ya kamata kowace macen aure ta wanke zuciyarta.

Sai dai Kudirat ta yu watsi da rade-radin da ake yadawa cewa kowace ‘yar fim na da ubangida da ake kira da ‘Sugar Daddy

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button