Labarai

Ina Ganin Babu Wani Abin Kuskure Idan Mace Ta Fara Cewa Tana Son Namiji

Ina Ganin Babu Wani Abin Kuskure Idan Mace Ta Fara Cewa Tana Son Namiji

Daga Fadila H. Aliyu (Golden Pen)

Ni da kaina da wasu mutane kusan kaso casa’in da biyar bisa ɗari mun yarda namiji kaɗai ne ya dace idan yaga macen da yake so zai iya ya same ta ya faɗa mata babu laifi kuma ba abin kunya bane.

Lokaci da dama nauyin baki na ja ma mata da yawa su kasa samun namijin da suke so wasu har ƙarshen rayuwar su.

Yayin da mace ta ga wani salihi mutumin kirki ƙilan wurin aikin sune ko abokin Yayan ta ko Malamin ta ko wani abokin hulɗa namiji mutumin kirki sai ta ga kamar ci baya ne ta furta tana son sa bare tayi wani yunƙurin da zai sa ta mallake shi.

Saɓanin namiji da zai iya ƙoƙarin sa domin mallakar wacce yake so idan ba a dace ba zai ƙara gaba ya nemi wata, ke ma babu inda aka hana ki, kika sani ma ko kece da kan ki za ki yi yunƙurin samun abokin rayuwa na dindin, idan ke kika gan shi kika zaɓa za ki iya jurewa a yi ta rayuwar cikin rufin asiri.

Nana Khadija RA ita ta fara ganin Manzon Allah SAW tace tana son sa, suka yi aure da tarin zuriya mai albarka, don me wani zai saƙa maki abinda ba haramun ba ya zama abin kunya, shi kaɗai ne zaki iya rayuwa da shi tal babu ƙari, idan kun haɗu ki faɗa masa kina son sa Allah zai shiga lamarin ki idan kin yi domin sa, ki duba cancanta ba laifi ba ne.

Kina ta doguwar addu’a kina neman miji nagari yana ta giftawa ta gaban ki me kike jira ne? Sai yayi wuf da wata kina nan zaune. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu