Labarai

Gwamna Masari Ya sake korar wani kusa a gwamnatinsa

Gwamna Masari Ya sake korar wani kusa a gwamnatinsa.

Gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Belli Masari ya sanar da sauke Alhaji Babangida Mohammed Nasamu data mukaminsa na shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Katsina Sema.

Bayanin hakan na kunshe be a cikin wata sanarwa daga sakataren gwamnatin jihar Katsina Alhaji Munatari Lawal da Manuniya.com ta samu kwafi a Katsina.

Takardar korar
Sabarwar ta sanar da cewa Gwamna Masari ya amince da nadin Haruna Musa a matsayin sabon shugaban hukumar Sema.

Kazalika, sanarwae ta ce Gwamnna Masari ya kuma sake ba da nada Sani Danlami a matsayin kwamishina a gwamnatinsa.

Sanarwar ta ce an kuma sauya wurin aiki ga kwamishinan kasa da safiyo Usman Nadada da aka mayar da shi zuwa ma’aikatar ayyuka na musamman. Sai kwamishinan matasa da wasanni Bashir Gambo Saulawa da aka mayar a ma’aikatar kasa da safiyo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu