Labarai

Adadin wadanda suka mutu a girgizar kasar Turkiyya da Syria ya kai 12,000

Adadin wadanda suka mutu a girgizar kasar Turkiyya da Syria ya kai 12,000

Girgizar kasa da ta afku a kasashen Turkiyya da Siriya ta yi sanadiyar mutuwar mutane 12,000 ya zuwa ranar Laraba yayin da ake ci gaba da neman ceto.

Girgizar kasa mai karfin awo 7.8 da 7.5 a ranar 7 ga watan Fabrairu ta afku a kudu maso gabashin Turkiyya kusa da kan iyaka da Syria.


Hukumar kula da bala’o’i, AFAD ta ce gawarwakin da ba a iya tantance su ba za a binne su cikin kwanaki biyar ko da ba a bayyana sunayensu ba.

Hukumar ta bayyana cewa za a yi wa irin wadannan mutanen bayan gwajin DNA, da daukar hoton yatsa domin tantancewa a nan gaba.


A yayin ziyararsa zuwa “birnin tanti” a Kahramanmaras, shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya yarda cewa an samu gazawa wajen mayar da martani na farko ga bala’in.


Shugaban ya sha alwashin cewa ba za a bar kowa a kan tituna ba, yana mai tabbatar da cewa an shawo kan matsalolin da aka fuskanta a yanzu.


Shugaban babbar jam’iyyar adawa ta Turkiyya Kemal Kilicdaroglu ya ce “Idan akwai mutum daya da ke da alhakin wannan, to Erdogan ne.”

Ma’aikatan agaji daga kasashe sama da ashirin sun shiga cikin dubun dubatar ma’aikata a yankin da girgizar kasar ta afku.


A arewacin Siriya, an gano wata jaririya, wadda ita kaɗai ta tsira daga danginta, a ƙarƙashin tarkace yayin da take manne da mahaifiyarta da ta mutu bayan haihuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu