Labarai

Babu Wanda Ya Bani Kyautar Gida Ko Mota Tun Bayan Ibtila’in Da Ya Same Ni, Cewar Rarara….

Babu Wanda Ya Bani Kyautar Gida Ko Mota Tun Bayan Ibtila’in Da Ya Same Ni, Cewar Rarara….

Fitaccen mawakin siyasar nan, Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (RARARA) ya musanta jita-jitar da ake yi na cewa an bashi kyautar Motoci da Gidaje, bayan wani iftila’i da ya fada masa.

Tun a ranar 20 ga watan Maris ne dai mawakin siyasar aka samu wasu fusatattun matasa da suka ɓuge da murnar cin zaben Abba-Gida-Gida suka kai farmaki Rarara suka ƙone masa motoci tare da sace kayan gidan.

Wanda tun bayan hakan wasu labarai a kafafaen sada zumunta ke ta yawo cewa wasu ƴan siyasa sun yiwa mawakin kyautar motoci da gidaje.

Sai dai a yau ne Rarara ya fito ya ƙaryata wannan labaran da wasu mutane ke ta yayayatawa a kafafaen sada zumunta, indai yai kira gare su da su daina ƙirƙirar abinda ba haka bane.

Mun gode sosai da sosai ku cigaba da bibiyar don samu Labarai Duniya da na Kannywood kasance da Manuniya.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu