Labarai

Allah Ya Yi Wa Dogariyar Yar Sandan Matar Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Zainab Shinkafi Bagudu, Sufeto Hassana Sule Rasuwa A Daren Alhamis Da Ta Gabata

Allah Ya Yi Wa Dogariyar Yar Sandan Matar Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Zainab Shinkafi Bagudu, Sufeto Hassana Sule Rasuwa A Daren Alhamis Da Ta Gabata .

INNALILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN

Dogariyar Matar Gwamnan Kebbi Ta Rasu

Allah Ya Yi Wa Dogariyar Yar Sandan Matar Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Zainab Shinkafi Bagudu, Sufeto Hassana Sule Rasuwa A Daren Talata Da Ta Gabata, Bayan Ƴar Gajeruwar Rashin Lafiya.

An Yi Jana’izarta Kamar Yadda Addinin Musulunci Ya Tanada A Jihar Kogi.

Allah Ya Jiƙanta Da Rahama!

HIKIMOMIN DA AZUMI YA ƘUNSA

Man in white thobe bowing down on the floor

Tambaya:
Assalamu Alaikum. Don Allah Malam a taimaka min da bayani game da dalilin da yasa ake yin Azumi?

Amsa:
Wa alaikum assalam. Azumi ginshiki ne daga cikin turakun Musulunci, waɗanda addinin Musulunci ba zai cika ba sai da su. Allah da Manzonsa sun yi umarni da shi, saboda wasu muhimman manufofi, ga wasu daga ciki:

1. Samun tsoron Allah, saboda mai Azumi yana barin abin da yake so saboda Allah, hakan zai sa ya ƙara samun tsoron Allah.

2. Samun kariya daga Shaiɗan, saboda Azumi yana takure hanyoyin Shaiɗan, wannan yasa zunubai suke ƙaranci a Ramadan.

3. Tuna talakawa da wahalar da suke ciki, saboda duk lokacin da mai kuɗi ya ɗanɗana yunwa zai tuna halin da talakawa suke ciki.

4. Sabawa rai wajen barin abin da take so, da kuma haƙuri akan abin da take sha’awa.

5. Kankare zunubai da kuma samun ɗaukakar daraja, saboda Azumi yana gyara zuciya, da kuma rai.

6. Samun lafiyar Jiki, saboda Azumi yana kariya daga cututtuka masu yawa, kamar yadda likitoci suka tabbatar.

7. Ta hanyar Azumi mutum zai saba da yin aiki don Allah, saboda AZumi sirri ne tsakanin Allah da bawansa.

Allah ne mafi sani.
29/01/2013

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu