Labarai

Budurwa ta Yiwa Wani Matashi Asiri Bayan ya Dirka Mata Ciki Ya Musanta, Ya Koma Tsince-Tsince.

Budurwa ta Tafkawa Matashi Asiri Bayan ya Dirka Mata Ciki Ya Musanta, Ya Koma Tsince-Tsince.

Wata mata ‘yar Najeriya ta labarta abun da ya faru da tsohon saurayinta wanda ya dirka mata ciki gami da musanta hakan shekaru da suka shude Matashim daga jihar Akwa Ibom wanda makwabcin goggonta ne shekaru 15 da suka shude, ya dirka mata ciki tana shekarar farko a makaranta Musanta cikin da yayi ne yasa ta zubar tare da tafkawa matashin mugun asiri wanda aka yi amfani da jininta aka yi.

Wata mata ‘yar Najeriya tazo soshiyal midiya da su bata shawarar yadda zata taimaki tsohon saurayinta wanda ke cikin tsananin rayuwa. Yayin bada labarinsu tare da sakaya suna a wani guruf a Facebook, matar ta bayyana yadda matashin wanda ‘dan asalin Akwa Ibom ne ya dirka mata ciki shekaru 15 da suka shude tare da musanta hakan.

Taje hutu gidan goggonta inda ta hadu da mutumin, wanda makwabcinta ne. A lokacin tana shekarar farko a jama’a, sun tsuduma kogin soyyaya gami da fara fahimtar juna. Sai dai yayin da rabo ya shiga tsakaninsu, matar ta bayyana yadda ya musanta dirka mata ciki har yayi barazanar sawa a daure ta.

Martanin da tsohon saurayintan yayi ya matukar bata mamaki. Daga bisani, wata kawarta ta hada ta da wani mai kemis wanda ya taimaka mata wajen zubda cikin. Matar ta ce cike da radadi tayi masa miyagun addu’oi, sannan ta manta da komai ta cigaba da rayuwa…

Matar ta yafe mata bayan wasu watanni da ya nemi gafararta. Sai dai, matar bata ji dadin halin da yake ciki yanzu ba. Duk da tayi aure da ‘ya’ya biyu.

Ta ce sun hadu a farkon shekarar 2022, inda taga duk ya susuce, ba mata bare ‘ya’ya.

“Ya shaidamin cewa, an fada masa nice tushen matsalarsa, na ce masa ni na dade da yafe masa har zuciyata. Amma ganinshi a wannan yanayin ya sani zubda hawaye.”

Kamar yadda ta rubuta

Martanin jama’a

Chiagozie Okwuaka ta ce

Kiyi masa addu’a. Ki roki Ubangiji ya aurar dashi to ya bashi yalwar dukiya. Shi dake yawan yafiya zai yafe masa. Ubangiji ya yafe miki, don me har yanzu kike rike dashi tsawon wadannan shekarun?”

Kate Onyegwara Okoli ya ce:

“Ba ke bace sanadiyyar tabewarsa. Tsumagiyar zaluncinsa ne ke zibgarsa. Ta yuwa yayi hakan ga wasu mata, amma muma mata ya kamata mu daina yin ciki ba tare da aure ba.

“Idan har se kayi, ta rika tunawa da ana siyar da maganin hana daukar ciki da kwaroron  roba”

Agulue Valentine ta ce: “Kina so in koma garesa ne ko ki bashi kyautar daya daga cikin ‘ya’yanki, don magance laifin da kike ganin naki ne. “Ki manta dashi sannan ki rika sanya shi a addu’a. Wasu matan, a koda yaushe ina cewa, ana saurin amsar addu’arsu. Idan ka cutar, ita kuma bata da hakki, alhaki zai farauto ka.”

Damola Paul ya ce:

“Babu abun da kika jawo… Mugun halinsa ya jawo masa. Ba ke kadai ya cutar ba a wannan rayuwar. Ko dai wani daban ya masa miyagun addu’oi ko kuma alhaki yayi maganin shi. Kin riga kin yafe masa, ki manta da shi ki cigaba da rayuwa, kada ki bari yasa kiji a ranki ko kina da laifi.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button