Labarai

Mijina Ya Takura Min Mun Saduwa A Ramadana cewar wata Matar Aure Ina Mafita

Mijina Ya Takura Min Mun Saduwa A Ramadana cewar wata Matar Aure Ina Mafita.

Mallam don Allah a taimaka min da mafita, Allah ya sanya wa zuri’arka albarka.

GA VIDEO DA MALAM YA BATA AMSA 👇

Mallam ya bata ansa a saukake, ga yarda Mallam ya bata ansan, ya ce;

“‘Yar’uwa mutukar yadda kika siffanta, haka abin ya faru, to ke babu kaffara a kan ki.

” Dalili kuwa shine ke takura miki aka yi, kuma ba ki da laifi a wajen ubangiji Allah.

“Amma gaskiya shi mijin naki ya saba wa Allah, kuma ya keta alfarmar watan Ramadana, toh dole ne ya yi kaffara, ta hanyar ‘yanta kuyanga, in bai samu ba sai ya yi azumi sittin a jere.

“Kamar yadda ya zo a hadisin Bukari mai lamba ta:616, idan bai samu dama ba sai ya ciyar da miskinai sittin, Allah ne mafi sani.

Wata baiwar Allah ta sake yiwa Mallam tambaya kamar haka;

“Malam ina cikin saduwa da mijina a cikin wannan wata na Ramadana, sai muka ji kiran sallar assalatu, me ye hukuncin azuminmu?

‘‘yar’uwa mutukar kuna jin kiran sallar, kun yi hanzari da sauri kun datse saduwar da kuke yi, to azumin ku yana nan.

“Amma in har kun ci gaba da yi ne koda na second daya ne, to azuminku ya karye, kuma za ku yi kaffara ku duka, idan kuma kin yi masa biyayya ne, shi kuma ya takura miki, to zai yi kaffara shi kadai. A duba Almugni: 3/65 domin karin bayani.

Allah ne mafi sani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu