Labarai

Kugiyar: NUT Na Adawa da cire Tallafin Man Fetur A Najeriya

Kugiyar: NUT Na Adawa da cire Tallafin Man Fetur A Najeriya.

Ƙungiyar Malaman Makaranta ta ƙasa a Najeriya ta ce tana adawa da shirin cire tallafin man fetur a ƙasar.

Shugaban ƙungiyar na ƙasar ne ya bayyana haka ranar Litinin a Abuja babban birnin ƙasar a lokacin taron ƙungiyar na ƙasa

Ya yi kira da a jinkirta aiwatar da cire tallafin man fetur ɗin.

Gwamnatin tarayyar ƙasar ta ce za ta daina biyan tallafin man fetur zuwa ƙarshen watan Yuni, kasancewar naira tiiliyan 3.36 ne kawai gamnatin ƙasar ta sanya a kasafin kuɗin ƙasar domin biyan tallafin wata shidan farko na shekarar 2023.

To sai dai shugaban ƙungiyar malaman ya ce matsalar tsadar man da za a fuskanta za ta ƙara hauhawar farashin kayyaki a ƙasar.

Ya ƙara da cewa ƙungiyar sanya ƙafar wando ɗaya da jihohin da suka ƙi aiwatar da sabon tsarin mafi ƙarancin albashi na 30,000 ga malaman makaranta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu