Kannywood

Hira ta musamman tari da babban darakto a kannywood Falalu A. Dorayi da zai mutukar baku mamaki

Ya kake ji idan aka zage ka ?

Gaskiya ina jin haushi. Kuma ban ma so naga an zage ni

Akwai wani lakabi da ake maka ?

Eh, suna da yawa. A can gida ina da suna wanda yake na fitar drama da nakeyi kafin nazama dan fim, na fara da wasan dabe ne. Wasan dabe kuma dole sai kana da sunan da ake kiran ka dashi. Wanda ana kirana “Dan aiyu” wanda bayan na zama dan fim, kusan “Baba” tafi karfi ga duk wanda yasanni a kannywood yanzu.

Ka taba yin fada da dambe ?

Eh to, dambe yana da fassarar sa daban , fada ma yana da fassarar sa daban. ban taba yin dambe ba, amma idan fada ne nayi.

Da wa kayi ?

Ah, da dama. Saboda kusan kafin inshigo industry ai nayi farauta. To ma farauci kuma zaka raba shi da fada?

DM nawa kake samu a rana ?

DM,DM,DM… To bazaka rasa DM ba. Ni gaskiya nakan samu amma da yake ni ba jarumi bane, jarumai su sukafi samun yawan DM. Mu daraktoci sai ‘yan gaisuwa da baza a rasa ba. Kakan samu DM biyar, shida, bakwai zuwa goma haka.

Yan matanka nawa ?

Kaii, ‘yan mata kuma? Hahaha, a’a bani da ‘yan mata gaskiya.

Me ke sa ka nishadi ?

To, abubuwan dake sa nishadi na da yawa, zama da family n’a sa nishadi, kuma ni ma’abocin kallon amerikan fim ne gaskiya.

Ka iya girki ?

Eh to na dan iya abu biyu acikin girki, na iya dafa shinkafa da wake, sannan na iya dafa taliya(Indomi, spaghetti…) Iya wannan kawai na iya.

Kana taya matarka girki ?

Tayawa shine abin da yashafi yara. Nakan taimakamata harkar yara, amma ba abin da ya shafi shiga dakin girki ba gaskiya.

Wace ce budurwarka ta fari ?

Budurwata ta farko… Kawai adai kyale maganarta. Ta ruga ta yi aure kuma yanzu zanshiga sabon babi na rayuwa. Bai kamata a taso gurin ba.

Lissafo mawaka biyar da kake son wakokin su ?

To… Ina son Shata, ina son Sani Sabulu, Ajinu, a yanzu kuma ina sauran Rarara, dakuma Naziru Sarkin Waka.

Wace jaha kafi so a Najeriya?

Gaskiya nafi son jahar Kaduna.

Me yasa Kaduna ?

Gaskiya Kaduna ni ina zaune a cikinta ina jin farin ciki. Ka zo na zo, baka isa kayimin kure ba sabanin sauran jahohinmu n’a arewa dazakaga damutum ya zo sai kaji ana ai ba asalin dan garin bane. Kaduna baza ace maka kai ba asalin dan garin bane saboda daman kuma din ba ‘yan garin bane.

Yin wasa ko bada umarni ?

Ko da yaushe ina bayan kemara. Nafi son daraktin Dina akan zama jarumi.

Arziki ko talauci ?

La ilaha illallahu ! Waye zai so talauci annabi ya ce mu nemi tsari da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button