Labarai

NNPP Ce Mafita Ga Yan Nijeriya Inji Haj Farida Barau

NNPP Ce Mafita Ga Yan Nijeriya Inji Haj Farida Barau.

Uwargidan dan takarar gwamnan jihar Katsina a jami’iyyar NNPP Haj Farida Mohammed Barau ta ce jam’iyyun PDP da APC duk sun ba ‘yan Nijeriya kunya domin ba su tsinana komai ba a kasar nan, illa ci baya.

Hajiya Farida Mohammed Barau ta ce jam’iyyar NNPP ta zo da tsare-tsare na cigaban mata, matasa da sauran al’ummar jihar Katsina da ma Nijeriya bakidaya.

Ta kara da cewa ko a lahira idan an shiga aljanna babu tsintsiya babu lema, sai dai kayan marmari, a don haka ne take kira gare su da su zabi wannan jam’iyyar.

Mun gaji da handama. Mun gaji da karairayin ‘yan siyasa. An yu muku alkawurra, shin ana cika muku, me ya sa, saboda baku san ‘yancin kanku ba ne? To yanzu ‘yancin kanku zai bayyana. Ku dangwala wa Engr, Sen Rabi’u Musa Kwankwaso domin sabuwar Nijeriya.

Ta ce mata na da gudunmuwar da suke badawa da kaso mai tsoka, don haka ya kamata su zabi wanda ya san mutuncinsu kuma zai kare musu ‘yancinsu.

Ta ce Engr Nura Khalil ya dade yana ba da gudunmuwa ga cigaban al’umma, duk kuwa da bai saci kwabon kowa ba.

An gwada PDP an shiga uku, an gwada APC an ida shiga uku. Ku gwada wannan jaririyar jam’iyya mai taken NNPP mai alamar kayan marmari. Kada ku biye wa Naira dubu, ko sabulu, ko taliya ko gishiri ku dawo ku na bin mu, mu taimake ku. Ku zo ku shiga jirgin Annabi Nuhu.

Mai dakin Engr Nura Khalil din ta yi takaicin cewa ‘yan siyasar da ke rike da mukamai daban-daban, na tserewa da iyalansu zuwa kasashen waje domin rayuwa mai inganci, an bar ‘ya’yan talakawa cikin kangin rayuwa.

Haj Farida Barau ta shawarci mata da matasan jihar Katsina da su zabi Engr Nura Khalil da sauran duk ‘yan takarar jam’iyyar NNPP domin su na da tsare-tsare da kudirori na cigaban al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu