Labarai

Mutumin da ya auri mata biyu ya bayyana cewa kamar a aljanna yake jin kansa saboda dadi

Mutumin da ya auri mata biyu ya bayyana cewa kamar a aljanna yake jin kansa saboda dadi

Wani matashi mai suna Umar Sani da ya auri mata biyu a rana guda a garin Minna na jihar Neja ya ce ya na ji kamar ya na aljanna.

Sani, wanda ya auri Safina da Maryam a ranar Juma’a, ya shaida wa wata jarida ta yanar gizo da ke Minna, Tsalle Daya, cewa “Ina jin kamar an ba ni gida a aljanna, ina godiya ga Allah matuka, kuma farin ciki na da nake ciki ba zai musaltu ba.

“Na gode wa Allah da farin ciki na auri mata biyu a lokaci guda. Dukansu suna da fahimta, kuma ina godiya da hakan.

“Mutane da yawa sun yi tunanin cewa za a sami matsala daga ɗayar su, amma Allah cikin hikimarsa, ya sa abubuwa su ka kasance daidai.”

Umar ya bayyana cewa ya yi auren ne saboda shima da ga gidan mata sama da ɗaya ya fito.

“Tun ina dan shekara 10, na ga mahaifina yana da mata hudu kuma na ga yadda suke zaman lafiya. Na yi wa kaina alkawari zan auri mata fiye da daya idan na samu hali, ko in yi aure uku ko hudu a rana guda.

Ko da yake ya ce iyayensa sun yi mamakin shawarar, amma ba su hana shi cika burinsa ba.

“Iyayena sun yi mamaki domin ko mahaifina bai auri mata biyu a rana daya ba. Amma ba su yi adawa da hakan ba. Abu mafi muhimmanci a gare mu a yanzu shi ne mu samu zaman lafiya,” inji shi.

Mun gode sosai da sosai ku cigaba da bibiyar don samu Labarai Duniya da na Kannywood kasance da Manuniya.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu