Labarai

Hukumar Yan Sanda Sunyi Ramda Pasto Bayan Hawa Mumbari Da Bindiga AK-47 A Abuja

Hukumar Yan Sanda Sunyi Ramda Pasto Bayan Hawa Mumbari Da Bindiga AK-47 A Abuja

Yanzu haka Fasto Uche Aigbe na majami’ar House on the Rock dake Abuja, yana tsare a hannun rundunar ‘yan sandan birnin tarayya sa’o’i 24 bayan ya hau  mumbari da bindigar AK47 a ranar Lahadi.

Wata majiya ta shaidawa Jaridar MANUNIYA cewa faston ya isa ofishin ‘yan sanda na babban birnin tarayya Abuja a ranar Litinin tare da jami’an dan sanda, Musa Audu wanda ya karbo bindigar da ya hau  kan mimbari da ita.

Majiyar ta ce an tsare  faston da dan sandan aka tafi da shi gidansa domin bincike.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda a babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, tace ‘yan sandan na kan gudanar da bincike, inda ta yi alkawarin cewa nan gaba kadan za’a fitar da sanarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu