Labarai

Mutum hudu sun jikkata yayin da Peter Obi ya yi Allah wadai da harin da aka kai kan magoya bayansa a Legas

Mutum hudu sun jikkata yayin da Peter Obi ya yi Allah wadai da harin da aka kai kan magoya bayansa a Legas

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi ya yi Allah-wadai da harin da aka kai wa magoya bayansa yayin da yake gudanar da taron sa a Legas ranar Asabar.

Daya daga cikin magoya bayan jam’iyyar Labour da suka jikkata ana jinya.

Magoya bayan Obi hudu sun samu raunuka a tsibirin Legas yayin yakin neman zabensa a dandalin Tafawa Balewa (TBS) ranar Asabar.

Da yake maida martani kan wannan Obi ya yi Allah wadai da harin, yana mai cewa bai dace ba.

Obi ya ce “Na samu rahoton cewa an kai wa wasu ‘yan uwa 4 hari tare da jikkata su a Legas gabanin taron na yau. Wannan lamarin, wanda aka shirya ko a’a, yana da matukar damuwa. An yi Allah wadai da irin wannan aikin.


“Ba za mu iya ci gaba da lamuntar hare-haren da ake kaiwa ‘yan adawar siyasa ba, wanda galibi ke kara ruruwa sakamakon kalaman batanci na shugabannin siyasa. Sabuwar Najeriya da muke nema, ita ce wacce aka kafa ta akan zaman lafiya da adalci, da mutunta doka.


“Ina kira ga hukumomin tsaro na jihar Legas da su kamo wadanda ke da alhakin kai hare-haren.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button