Labarai

Yau Ranar Masoya: Hukumar yaki da AIDS a Najeriya Ta Shawarci Matasa Su Guji Wuce Gona da iri

Yau Ranar Masoya: Hukumar yaki da AIDS a Najeriya Ta Shawarci Matasa Su Guji Wuce Gona da iri.

Hukumar yaki da cuta mai karya garkuwar jiki ta Najeriya ta gargadi matasa da su gu ji sharholiyar da za ta iya kai su ga hadarin kamuwa da cutar.

Shugaban hukumar da ake kira NACA a takaice, Gambo Aliyu, shi ne ya yi gargadin ga jama’a musamman matasa, a jiya Litinin.

A sakonsa na ranar masoya da ake kira Valentine’s Day na wannan shekara, shugaban ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan lokaci su yi gwaji domin sanin matsayinsu dangane da cutar ta HIV/AIDS.

Aliyu ya shawarci matasa da su yi bikin cikin nuna so da kauna da kare masoyansu daga duk wani abu da zai iya cutar da su, sannan su guji aikata abin da zai iya kai su ga kamuwa da cuta mai karya garkuwari jiki da sauran cutuka na jima’i.

Shugaban ya ce, a wannan lokaci na bikin ranar ta masoya ta duniya ana samun yawan abubuwa barkatar na saduwa da sauran dabi’u tsakanin maza da mata da kan iya kai su ga wani yanayi na nadama.

A duk shekara rana irin ta yau 14 ga watan Fabarairu ake bikin Ranar Masoya a duniya, wadda ake kira Valentie’s Day.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button