Labarai

Sabuwar Naira: Emefiele ya gana da Muhammadu Buhari bayan umarnin kotun koli.

Sabuwar Naira: Emefiele ya gana da Muhammadu Buhari bayan umarnin kotun koli.

Sa’o’i kadan bayan da kotun kolin kasar ta dakatar da babban bankin Najeriya CBN daga aiwatar da wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu na tabbatar da ingancin kudin tsohon naira, gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

MANUNIYA ta tuna cewa kwamitin mutum bakwai na kotun koli karkashin jagorancin mai shari’a John Okoro, a wani hukunci bai daya da ya yanke a ranar Laraba ya bayar da umarnin ci gaba da aiki da tsofaffin kudaden naira koda bayan sabon wa’adin. Wannan ci gaban ya biyo bayan takardar da gwamnatocin jihohin Kogi, Kaduna da Zamfara suka shigar ranar Talata.

Kotun kolin ta kuma bayyana cewa, gwamnatin tarayya da na CBN ba za su ci gaba da wa’adin da za a yanke hukunci a ranar 15 ga watan Fabrairu ba.

Har yanzu ba a san sakamakon taron ba amma kamar yadda gidan talabijin na Channels TV ya ruwaito, ziyarar ta shugaban bankin na da alaka da hukuncin kotun koli.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu