Labarai

Dan Sholi Ya Bayyanawa Rakiya Musa Soyayyar Sa Bayan Jin Abun Da Ya Faru Da Ita

bayan kallan cikakken video hirar Jaruma hadiza gabon da rakiya Musa shahararran Dan wasan barkonci wanda akafi SANI da Dan sholi ya bayyanawa Rakiya musa budaddiyar wasika ta soyayya.

Magunguna.

Abubuwan da ruwan kokwamba yake karawa a jikin dan adam daga Namiji har Mace

Ruwan kokwamba ya zama sanannen ruwan sha ga masu son gyaran jiki, amma ba hakan yake ba a wajen gama garin mutane sanadiyar rashin sanin fa’idar ruwan wajen kiwon lafiya managarciya.

Ga kadan daga cikin hanyoyi da ruwan kokwamba zai amfani jikin dan’adam.

Yalwar ruwa a jikin dana’dam: Ruwa wani muhimmin jigo ne wajen gudanar da al’amuran jikin dan’adam ta yadda idan babu ruwa a jikin mutum zai tagayyara ya lalace.

Adadin ruwa da ya kamata ace mutum ya sha a kullum ya na danganta ne da yanayin jiki zuwa jiki.

Kofi shi zuwa takwas na ruwan kokwamba zai samar da wadatacciyar lafiya a jikin dan’adam duk da sanin cewa, ruwa wani abu ne da yake gundurar mutum da zarar ya koshi.

Amma ruwan kokwamba zai sanya mutum ya yi ta neman karin abinci sabida dandanon shi da ya banbanta da na ruwa.

Hana nauyin jiki: Ga duk wani mai son rage nauyin jikinsa to ya dunga yin amfani da ruwan kokwamba ya na da matukar taimakawa wajen inganta hanyoyin narkar da maiko a jikin dan adam.

Sau tari mutum zai rasa gane cewa yunwa yake ji ko kuma kishi ta yadda mutum zai gane haka shi ne, ya samu kofi daya na ruwan kokwamba mai sanyi ya fara sha idan yunwar ta gushe to daman kishirwa ce kawai, amma idan yunwar ba ta gushe ba to lallai mutum zai gane cewar yunwa ce ke damun sa kuma sai ya nemi abinci.

Hana yaduwar cutar daji wato kansa: Kokwamba tana taimakawa wajen hana kamuwa da cutar daji sandiyar sunadaran cucurbitacins da lignans, wadanda suke hana kamuwa da cutar kansa wanda wasu ke kiran ta da suna cutar daji.

Amfani da ruwan kokwamba yana rage yaduwar cutar kansa da take kama ‘yayan maraina na mazakutar namiji.

Rage hawan jini: Yin amfani mai yawa da gishiri wanda yake kunshe da sinadarin sodium, yana assasa gamuwa da cutar hawan jini.

Ita kuwa kokwamba tana dauke da sinadarin potassium wanda yake wanko duk wani sinadarin na sodium daga cikin kodar mutum, wadda daman ita ce mai rarraba amfani na duk wani nau’in abinci da mutum yaci.

Gyaran fata: Ruwan kokwamba yana sanya fata ta yi kyau fyas-fyas domin ga mai shan ruwan kokwamba ko da yaushe jikinsa zai zama cikin wadaceccen ruwa don daman bushewar fata ita ke sanya fatar dan adam ta lalace.

Ruwan kokwamba yana hankado duk wani dafi ko gubar da take jikin fatar dan adam kuma kokwamba tana da sinadarin bitamin B-5, wanda yake magance kurajen fuska.

Domin haka sai mu dage da shan ruwan kokwamba domin samun cikakken lafiya yadda ya kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu