Labarai

Matar Da ta Nemi a Sake Ta Don Mijinta Ya Hana Ta kudi Tayi Birthday A Kano

Matar Da ta Nemi a Sake ta Don Mijinta Ya Hana ta kudi Tayi Birthday A Kano.

Matar da ta nemi a sake ta don mijinta ya hana ta kudin ‘Birthday’ a Kano.

An maka wata sabuwar amarya mai suna Fatima Bashir da aka fi da ‘Yar Albarka a kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a Post Office, Kano bisa zarfs n kwaraya wa mijinta Alhaji Nura Gambo ruwan sanyi don ya ki ba ta kudin da za ta gudanar da bikin ‘birthday’ dinta.

Wannan mataki na wannan amarya, ya sa mijin ya fara makyarkyatar sanyi, da ya kamu da rashin lafiya.

Yan sanda da dai ne suka gurfanar da ‘Yar Albarka a gaban Alkali Nazifi Adam kan zargin keta hakkin dan’Adam da kuma tsoratarwa.

Lauyan mijin Badamasi Gandu, ya fada wa kotun cewa matar ta nemi mijin ya ba ta wasu kudi domin bikin zagayowar ranar haihuwarta, shi kuma ya ki ba ta, shi ne dalilin da ya sa ta nemi illata shi, kuma ta nemi ya sake ta.

Lauyaj ya sanar da kotun cewa idan har tana son ya sake ta, dole sai ta biya shi diyyar kudi Naira milyan 10 da ya kashe wajen aurensu.

Sai dai amaryar ta ki amsa laifinta, kotu kuma ta bayar da ita beli kan sharadin cewa har yanzu matarsa ce, sai kotun ta dage zaman sauraron karar zuwa ranar 3 ga Maris, 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button