LabaraiSiyasa

Yan Hamaiya Sun Yi Watsi Da Tsarin Gabatar Da Sakamon Zaben Najeriya

Wakilan jam’iyyun hamaiya sun yi watsi da yadda a ke gabatar da sakamakon zaben shugaban Najeriya a wuni na biyu da fara gabatar da sakamakon.

ABUJA — 

Dakin gabatar da sakamakon ya kusa hargitsewa da muhawara a lokacin da a ka baiyana sakamakon jihohin Kwara da Osun da kuma Ondo.

Wakilin jam’iyyar PDP, Dino Melaye, shine akan gaba a nuna sam ba a bin ka’ida wajen baiyana sakamakon don ba a gabatar da ainihin sakamakon da a ka dauko daga jihohi.

Kazalika Melaye ya ce ya zama wajibi a rika nuna sakamako da na’urar BVAS mai hana magudi ta dauka tare da sakamakon takarda.

Shi ma wakilin jam’iyyar LP, Umar Ibrahim, ya ce ba za su yarda da tsarin gabatar da sakamakon ba, ya na mai zargin shugaban hukumar zaben Farfesa Mahmood Yakubu da daukar alkawarin duba korafi, amma karshe bai cika alkawarin ba.

Shugaban hukumar zaben mai zaman kanta, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bukaci kwantar da hankali da nuna cewa wakilin PDP na neman yamutsa zaman.

Za a cigaba da gabatar da sakamakon bayan hutun rabin lokaci da a ke tafiya.

Saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu