Labarai

Shugaba Buhari Ya Roki Daular Larabawa Ta Janye Takunkumin Hana Visa Ga Yan Najeriya

Shugaba Buhari Ya Roki Daular Larabawa Ta Janye Takunkumin Hana Visa Ga Yan Najeriya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci Hadaddiyar Daular Larabawa da ta dage takunkumin hana Viza da ta sanyawa ‘yan Najeriya.

Buhari ya kuma bukaci da a dawo da ayyukan kamfanin jiragen sama na Emirates da aka dakatar sakamakon gazawa wajen dawo da kudaden da suka makale a Najeriya.

Shugaban a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Mallam Garba shehu ya fitar, yayi wannan roko ne a ranar Talata yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban daular larabawa, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan.

Ya kuma yi nuni da cewa, an kawar da duk wata matsalar dangantaka da ke tsakanin kasashen biyu ta hanyar ofishin jakadanci da suka shafi halin wasu ‘yan Najeriya a kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button