Labarai

INEC Ta Bawa Tinubu Takardun shaidar zama A Matsayin Zababben Shugaban Kasa

Dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben shugaban kasa da aka kammala kwanan nan,

Bola Ahmed Tinubu a ranar Laraba ya karbi takardar shaidar cin zabe daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a matsayin zababben shugaban kasar Najeriya.

A safiyar Laraba ne aka bayyana tsohon Gwamnan Legas a matsayin wanda ya lashe zaben da jam’iyyun siyasa 18 suka fafata.

Ya doke Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, da Peter Obi na jam’iyyar Labour wanda ya samu matsayi na biyu da na uku.

Tinubu ya samu kuri’u 8,794,726 daga cikin jimillar kuri’u 24,025,940 da aka kada, kamar yadda babban jami’in zabe kuma shugaban INEC, Mahmoud Yakubu ya bayyana a lokacin da yake bayyana sakamakon zaben.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu