LabaraiSiyasa

Peter Obi Ya Lashe zaɓen Birnin Tarayya – Abuja

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya yi nasara a yankuna hudu daga cikin shida da ke babban birnin tarayya, Abuja da kuri’u masu rinjaye.  

Tun a ranar Lahadi dai Obi ske kan gaba wajen lashe yankin Bwari, Kuje, Gwagwalada da AMAC tare da kuri’u masu gwabi, yayin da APC ta samu nasarar lashe yankin Kwali da Abaji.

A sakamakon karshe da aka tattara, LP ta samu kuri’u 281,717 da ta kayar da dan takarar APC, Bola Tinubu, da ya samu kuri’u 90,912 sai kuma PDP ta samu kuri’u 74,193.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu