Labarai

Anya Ba Ahalul Kitab Zan Aura Ba Kuwa Adam A Zango Na Neman Shawara

Shahararren jarumi kuma mawaƙi a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood waton Adamu Abdullahi Zango yayi wani rubuta a shafinsa na facebook inda yace “anya ko ba Ahalul Kitab zashi auraba ?

Kamar yanda munka sani auren Ahalul Kitab aurene da musulmi yake auren wadda ba musulmaba kamar yanda addinin Musulunci ya aminta dayin hakan.

Jarumin yanemi shawara daga wajen masoyansa akan subashi shawara dangane da wannan lamarin.

Bayan neman shawarar masoyansa dake bibiyarshi a shafinsa na facebook, yaƙara sake wallafa hotun budurwa da keso ya aura wadda ba musulmaba. kamar yanda zaku ganin hotunta kai tsaye.

Sai dai wallafa hotunta dayayi akaro na biyu yayi rubutu inda inda yake cewa, munafukai zasu cewa haɗin nasu baiyiba.

Adam A Zango Ya bayyana cewa yataɓa soyayya da wata wadda ba musulmaba a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood amma aurensu baiyiba a wata hira da akayi dashi da Jaruma Hadiza Aliyu Gabon.

Idan bamu mantaba kwanakin baya da suka gabata shahararen jarumin nan ya saki matarsa inda yafito a social media ya bayanawa mutane cewa bazai sakeyin aureba.

Yafaɗi hakanne saboda irin cecekuce da mutane keyi dangane da abinda yashafi aurenda yakeyi dayawa. Inda mutane dayawa suke ganin kamar yana yawan auri saki.

Hakan za tunzura jarumin hartakai yayi iƙirarin cewa bazai sakeyin aureba. Amma bisani masoyansa sunbashi hakuri akan cewa yadaina biyema mutane Domin Allah kaɗai keyiwa mutane dai-dai.

Yanzu haka jarumin ya bayana cewa 17-03-2023 za’a ɗaura auren da baturiyar wadda ba musulmaba.

Munso muji wane gari ko ƙasa wannan baturiyar take dakuma sunanta amma bamu samu damar jin tabakinsaba.

Zamucigaba da kawomuku labarin yanda al’arin zai kasancewa atsakaninsu.

Amma kafinnan wace shawara zakaba jarumi Adam A Zango dangane da wannan lamarin ?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu