Labarai

Muna kan bakarmu na wa’adin daina amfani da tsohon kudi – Emefiele

Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya ce har yanzu suna kan bakarsu na wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu game da daina karbar tsoffin takardun kudi a fadin kasar.

Emefiele na bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi ga jami’an diflomasiyya na kasashen duniya a ma’aikatar harkokin wajen Najeriya da ke Abuja, babban birnin kasar.

“An fara samun sassaucin karancin kudin da ake fama da shi a sassan kasar, sakamakon karba da ake yi a banki wanda hakan ke nufin sabbin takardun kudi sun wadata, saboda haka babu dalilin kara wa’adin ci gaba da karbar tsoffin takardun kudi,” in ji Emefiele.

Wannan matakin dai ya kara jefa al’ummar Najeriya cikin rudani, bayan da kotun kolin kasar ta wa’adin zuwa ranar 15 ga watan Fabrairu, kafin ta yanke hukunci na karshe.

Yanzu haka dai ‘yan kasar sun sake shiga tashin hankali, yayin da bankuna suka ki karbar tsoffin takardun naira a rassansu da ke fadin kasar a ranar Litinin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button