Labarai

Kotun Ƙoli ta ɗage sauraron ƙara kan wa’adin daina karɓar tsoffin kuɗi

Kotun Ƙoli ta dage ci gaba da shari’ar musanyar takardun Naira na Babban Bankin Nijeriya, CBN, zuwa ranar Laraba 22 ga watan Fabrairu domin sauraren kararrakin da jihohi 10 suka shigar.

Kotun kolin da ta fara sauraren shari’ar a ranar Laraba, ta cika makil da wasu manyan lauyoyi da gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi, Nasir El-Rufai da Yahaya Bello.

A zaman da ya gabata, kotun ta dakatar da aiwatar da wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun kudi a ranar 10 ga watan Fabrairu na CBN kan N200, N500 da N1,000.

Jihohin Zamfara da Kogi da kuma Kaduna ne suka shigar da karar gwamnatin tarayya da kuma babban bankin kasa CBN.

Sauran jihohin da suka hada da Neja, Kano, Ondo, Ekiti, su ma sun maka CBN da gwamnatin tarayya a gaban kuliya kan batun daina amfani da tsofaffin takardun kudi.

An fara zaman kotun inda mai shari’a John Okoro ya jagoranci kwamitin mutum bakwai.

Ya ce bai kamata kotu ta yi watsi da shari’ar da kuma manufarta ba domin ta shafi ’yan Nijeriya da ke cikin mawuyacin hali.

Jihar Legas, ta hannun babban mai shari’a, Moyosore Onigbanjo, ita ma ta nemi shigar da karar gwamnati kan batun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu