Labarai

Dan Takarar Gwamnan Kano Gawuna ya taya al’ummar musulmi shigowa watan Ramadan

Dan Takarar Gwamnan Kano Gawuna ya taya al’ummar musulmi shigowa watan Ramadan….

Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya taya al’ummar musulmin Kano da ma kasar baki daya murnar shigowa watan azumin Ramadan.

Yayin da muka fara azumin watan Ramadan, Ina fatan zaku yi koyi da halaye ce da mu yi koyi da koyarwar Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) na tausayi, soyayya, hakuri, zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan watan Mai Alfarma.

Watan Ramadan wata ne da yake baiwa Musulmi damar Kara samun kusanci da Allah (S.W.T)”. A cewar Gawuna.

Ya kamata mu himmatu wajen yin amfani da wannan wata ta hanyar karfafa imaninmu da kuma bautar Allah S W T.

Ina rokon Allah ya karba mana addu’o’inmu a cikin wannan wata mai albarka, kuma yasa Muna cikin yan tattun bayi”. Inji Gawuna.

Gawuna ya kuma bukaci al’ummar Musulmi da sauran ‘yan Najeriya da su yi amfani da damar da aka samu na watan Azumin Ramadan wajen kara yin addu’o’i domin kara samun ci gaban zaman lafiya da ci gaban jiharmu da kasar baki daya.

Mun gode sosai da sosai ku cigaba da bibiyar don samu Labarai Duniya da na Kannywood kasance da Manuniya.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu