Labarai

Innalillahi kalli videon yadda aka samu hatsarin jirgin ruwa mutane dayawa sun mutu….

Yanzu-Yanzu: APC Tayi Amai Talashe Kan Korar Wasu Jiga-Jigan Jam’iyyar

Jam’iyyar All Progressives Congress APC mai mulki a daren ranar Lahadi ta nesanta kanta da zargin korar shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Kudu maso Kudu, Cif Victor Giadom da Sakatare Ita Udosen, inda suka bayyana matakin a matsayin wanda ya sabawa doka da oda,Punch ta rawaito.

An amince da tsige shugabannin APC a wani kuduri na musamman mai dauke da rattaba hannun mukaddashin shugaban kungiyar na shiyyar/Sakataren kungiyar na shiyyar, Blessing Agbomhere; Mukaddashin Sakatare/Jagora na Musamman na shiyyar, Cif Edet Ita Asia a Fatakwal ranar Asabar.

Sauran wadanda suka rattaba hannun sun hada da Ebimobowei Oyas, shugaban matasa na shiyyar da Mrs Cynthia Princewill, shugabar mata ta shiyyar.

An zargi Giadom da kin kiran taro da kuma kawo cikas ga duk wani yunkuri na kiran taron mambobin kwamitin zartarwa na shiyyar domin gudanar da harkokin siyasar yankin.

Kudurin ya kuma nuna mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar ya ki amincewa ko karbar korafe-korafe daga wasu Jihohin yankin.

Da yake mayar da martani game da faruwar lamarin, sakataren yada labaran jam’iyyar APC na kasa, Felix Morka, ya bayyana hakan a matsayin wanda ya sabawa doka kuma ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar, yana mai cewa wasu mutane da ba su da hurumin daukar wannan mataki ne suka aikata hakan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu