Labarai

Siyar Da Kadarorin Gwamnati Gada Nayi A Wajen Wadanda Suka Gabace Ni – Ganduje

Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da ya jagoranci bude sabon ginin ma’aikatar matasa da wasanni ta jihar Kano.

Na ji wani yana cewa wai ana sayar da gidaje, to Ina so ya sani gwamnatocin baya ma sun sayar, Kuma idan bashi da masaniya ya zo in nuna masa gidajen da mai gidan sa ko kakansa a siyasa ya siyar, da kuma wanda babansa a siyasance ya siyar.” Inji Ganduje.

Gwamna Ganduje ya yi suka Mai kaushi kan wannan batu na sayar da wuraren, sakamakon yadda lamarin yaji zuwa ba zato ba tsammani.

Ya kara da cewa Kwankwaso ma yayi amfani da damar sa a matsayin gwamna, wajen siyar da kadarorin da aka ganin na al’umma ne ga wasu na daban.

A don haka ne a cewar Ganduje aikata hakan ba laifi ba ne a gwamnatance, domin kuwa dama ce da kowa ne gwamna ke da ita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu