Labarai

Mahaifinku Bayero ya yi addu’a cewa ni ne shugaban Najeriya – Atiku ya fadawa Sarkin Kano

Mahaifinku Bayero ya yi addu’a cewa ni ne shugaban Najeriya – Atiku ya fadawa Sarkin Kano.

Related Articles

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya tunatar da mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero cewa mahaifinsa, Alhaji Ado Bayero, ya shaida musu a wata ziyara da ya kai fadar cewa shi (Atiku) zai zama shugaban kasa.

“Mun kai ziyarar ban girma fadar shugaban kasa a wani lokaci a lokacin da nake Mataimakin Shugaban Najeriya, marigayi Sarki Ado Bayero ya ce ya ga a cikinmu wanda zai zama Shugaban kasa kuma zai kawo daukaka a Najeriya,” in ji Atiku.

Atiku Abubakar ya kara da cewa marigayi sarki Ado Bayero bai tsaya a haka ba. Ya kuma ci gaba da addu’ar Allah ya baiwa shugaban kasar da ya gani ya kawo wa Nijeriya hayyacinta, ya kuma inganta zamantakewa da tattalin arzikinta.

Ya ce ya yi imanin cewa shi ne wanda Marigayi Sarki Ado Bayero ya ambata shi ya sa ya zama wajibi mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi koyi da shi tare da yi masa addu’a domin cimma burin Marigayi Bayero.

Atiku Abubakar, wanda ke Kano a kan yakin neman zabensa na shugaban kasa, ya kasance a fadar sarkin kasar a ziyarar ban girma, tare da mukarrabansa, ciki har da dan takarar mataimakinsa Ifeanyi Okowa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button