Labarai

Mage ta janyo musulintar dubun mutane a duniya Allahu akbar Labari Mai Ratsa Zuciya

MAGUN GUNA

Amfanin Shayi Da Goriba Ajikin Dan Adam

Ana kiran wannan itaciya da goruba a harshen Hausa, da turanci kuma ana kiranta da ‘Doum palm tree’ yayin da suke kiran ‘ya’yanta da ‘Doum palm Fruits’.

Itaciya ce mai tsohon tarihi da al’ummai daban-daban na duniya suka jima su na amfani da ita wajen samar da magungunan cutuka ma su yawa.

Misali masana sun ce tun fiye da shekaru 2000 kasar Sin ke amfani da ita don warkar da cutukan dake addabar bil adama.

Hakanan, mai karatu na sane da tsohon tarihin kasar Misra, wacce ita ma masanan su ka bayya cewa shekaru aru-aru da suka shuda suke amfani da goruba don samar da magani.

Kodayake, mu na cikin karni da ake bugun kirji da ci gaban zamani, saboda kirkire-kirkire, da nazarce-nazarcen kimiyya, amma duk da haka masana a wannan zamani sun gano irin rawar da goruba za ta iya takawa wajen samar da waraka ga wadansu cutukan dake addabar dan-adam.

Kafin mu fara bayyana irin amfani da ta ke da shi ga lafiyarmu, ga jerin sanadaran da binciken wannan zamani ya tabbatar goruba na kunshe da su.

Sanadaran su ne: Bitamin A, B da na C, sai sanadarin ‘Zinc’ da ‘Calcium, Kalium, Iron, Fibre, Protein, Glucose, Nitrogen, da kuma phosporos.

Bayan nazari mai zurfi da mujalla ta gudanar, ta samu nasarar ganowa tare da jero amfanin goruba guda goma sha biyar ga jikin dan-adam. Da fatan a sha karatu lafiya.

  1. Maganin Cushewar Ciki.

Kamar yadda mai karatu ya sani daya daga cikin hanyoyin da masana a fannin lafiya ke bayarwa domin mangance cushewar ciki ita ce, yawaita cin ‘ya’yan itatuwa,

musamman wadanda ke kunshe da wani sanadari na Fibre. Saboda haka, ɗaya daga cikin ‘ya’yan itatuwa da za ku iya ci mai dauke da wannan sanadarin mai yawa ita ce’ ya’yan itacen Goruba.

Allah Ya yiwa goruba baiwar wannan sanadari mai yawa Kamar yadda aka ambata a sama, saboda haka ne take da matukar fa’ida wajen warware wannan matsala.

  1. Magance Zafin Jiki

Yanayin zafi wani irin yanayi ne dake haifar wa mutum kasala da kuma zafin jiki, musamman a kasashe ma su zafi irin namu. Saboda haka, idan kuna neman wani abu da zai iya sanyaya jikinku sannan ku samu kuzari a lokacin zafi, to ‘ya’yan goruba su ne mafita.

A irin wannan yanayi da dan-adam ke da bukatar sanyaya jiki da kuma samun kuzari, ba’a bukatar hada ta da wani abu, za’a ci gorubar ne zallanta.

  1. Rage Yanayin Damuwa

Sau da yawa mukan fuskanci matsalolin da zasu iya haifar ma na da damuwa da ake kira ‘stress’ da turanci, sakamakon al’amuran da muke gudanarwa yau da kullum. To, idan dan-uwa ya tsinci kai a irin wannan yanayi lokaci ne da zai nemi goruba, musamman wacce aka tace ta aka yi lemonta.

Masana sun tabbatar da cewa shan ruwan goruba na iya kwantar da hankali cikin sauki.

Tuni nazari da masana suka gudanar ya tabbatar da cewa sanadarin bitamin C na taimakawa wajen rage matsalolin damuwa irin wadda mu ka ambata a sama.

Wannan ya sa yawan wannan sanadari na bitamin C da goruba ke kunshe da shi ke taka muhimmiyar rawa wajen magance wannan matsala.

Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa bai wa marasa lafiya dake fama da matsalar damuwa sanadarin bitamin C na matukar taimakawa wajen inganta yanayinsu.

4 Inganta Lafiyar Koda.

Ko mai karatu ya san amfanin koda a jiknsa ? Koda na daya daga cikin muhimman sassan jikinmu. Saboda Koda ce ke da alhakin tace wa tare da fitar da duk wani sanadari da ka iya cutar da jikinmu. Wannan dattin jiki da koda ke tacewa na fita ne ta hanyar fitsari. Akwai wani sanadari mai suna ‘Phosphoros’ a turance dake da yawa cikin ‘ya’yan itaciyar goruba da ke taimakawa wajen inganta lafiyar koda.

  1. Magance Kurajen Fata.

Kaikayi, radadi da damuwa ba su kadai ne illolin kurajen fata ba, a’a baya ga haka su kan yi lahani ga fatar jikinmu kwarai da gaske. To amma ‘ya’yan goruba na iya taimakawa wajen magance irin wannan matsala ta fata.

Ko da yake har zuwa wannan lokaci babu wani nazari game da hakan. Amma, wasu daga cikin masana, sun yi amannar cewa ‘ya’yan goruba na iya warkar da cututtukan dake shafar fatar dan-adam.

  1. Samar Da Kuzari Ga Jiki.

Mu na bukatar kuzari domin samun damar aiwatar da ayyukanmu na yau da kullum cikin kuzari da nishadi.

Ɗaya daga cikin tushen dake samarwa jiki kazar-kazar shine ‘sukari’. Ko da kwakwalwarmu takan gudanar da aikinta ne sakamakon samun sanadarin siga (glucose). Saboda haka ita kuma Goruba na kunshe da wannan sanadari.

  1. Gyaran Gashi.

Hakanan dai akwai nazari da aka gudanar wanda ke tabbatar da yadda wannan ‘yar itaciya ke taimakawa wajen tsirar gashi ga dan-adam.

Yadda za a yi domin samun wannan fa’ida shi ne, za a jika ta, sannan ake wanke gashin da wannan ruwan, da sannu za a ga biyan bukata.

8 maganin Basir.

Ga duk ma su fama da wannan matsala ta basir, mu na yi mu su albishir da yin amfani da goruba don samun sauki daga wannan matsala. Domin magance matsalar basir za’a yawaita cin ta ne ba tare da hada ta da komai ba.

  1. Maganin Hawan Jini.

Kamar yadda aka jero sanadaran da wannan ‘yar itaciya ta kunsa, haka wani nazari ya nuna tana taimakawa ma su fama da matsalar hawan jini.

Sai dai a nan an bada shawarar samun garinta, sannan a jika shi, bayan an tabbatar da ya jika sai a sha a kalla sau uku a rana.

10 Karfin Hakori Da Kashi.

Ba shakka yawan cin goruba na kara karfin kashi da na hakori. Ba don komai ba sai don an tabbatar da ta na kunshe da sanadarin ‘Calcium’ wanda ke da matukar muhimmanci wajen ginin kashi da karfinsa.

  1. Karawa Namiji Kuzari Yayin Jima’i.
  2. Riga-kafin kamuwa da ciwon Zuciya.
  3. Riga-kafin kamuwa da cutar daji.
  4. Ta na rage kiba da kitsen cikin jini maras amfani ga jiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Shiga WhatsApp Group Din Mu